Gwamnatin Jigawa za ta hada hannu da Saudiyya don inganta makarantun allo

Date:

 

Gwamnatin jihar Jigawa za ta haɗa hannu da gidauniyar ‘Alfurqan Qur’anic’ ta ƙasar Saudiyya don inganta makarantun tsangaya da ke faɗin jihar.

Cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran gwamnan, Hamisu Mohammed Gumel ya fitar, ya ce an cimma hakan ne bayan wata ziyara da shugaban gidauniyar, Sheikh Abdalla Ibn Nasir Al-Utaibiy, ya kai wa gwamnan jihar, Mallam Umar Namadi ranar Juma’a a gidan gwamnatin jihar da ke Dutse.

Talla
Talla

Sheikh Al-Utaibiy, ya ce manufar haɗin gwiwar shi ne zamanantar da hanyoyin karatun allo domin sauƙaƙa hanyoyin koyon karatun da kuma haddar Al-qur’anin mai tsarki.

Ya ƙara da cewa gidauniyarsa ta ƙware wajen amfani da hanyoyin zamani na koyon karatun alqur’ani da kuma sauƙaƙa koyar da shi ga masu lalurar ji (kurame) da ƙananan yara.

Jihar Jigawa na daga cikin jihohin ƙasar da ake tura ƙananan yara makarantun Allo na gargajiya da ake kira ‘almajirci’ domin samun ilimin alqur’ani.

Wasu iyayen kan tura yaran zuwa makarantun tsangayar ba tare da tanadar musu abincin da za su ci ba, inda a wasu lokutan yaran kan ƙare a bin gidajen mutane da kasuwanni da kan tituna suna barar abincin da za su ci.

Sanata Kwankwaso ya fitar da matsayarsa kan zanga-zangar tsadar rayuwa a Nigeria

Wani abu da masana da gwamnatoci ke ganin rashin dacewarsa, suna masu fargabar hakan ka iya jefa rayuwar ƙananan yaran cikin hatsari.

A nasa ɓangare gwamnan jihar jigawa, Mallam Umar Namadi ya ce gwamnatinsa na gudanar da wasu tsare-tsare don inganta makarantun tsangayar da ke faɗin jihar, ta hanyar haɗa wa yaran da ilimin boko da koya musu sana’o’in da za su dogara da kansu.

Talla

Ya ƙara da cewa gwamnatinsa ta gina manyan makarantun tsangaya na zamani a shiyoyin jihar uku, da nufin samar wa jihar malaman qur’ani masu ƙwarewar sana’o’in hannu, sannan suke da wayewa ta fannin ilimin boko.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bai dace ɗalibai su rika murnar kammala karatu ta hanyoyin da ba su dace ba – Mal Ibrahim Khalil

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa ‎ ‎ ‎Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano...

Budaddiyar Wasika ga Gwamnan Kano kan wanda zai maye gurbin Muhuyi Magaji R/gado daga Kungiyar Lauyoyi yan Kano

Zuwa ga Mai Girma Alhaji Abba Kabir Yusuf Gwamnan Jihar Kano Gidan...

Dan majalisa Bichi ya sake biyan kuɗin makarantar dalibai 121 masu karatun digiri na biyu da na digirin digirgir

Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Mazabar Bichi a Majalisar...