Daga Maryam Muhammad Ibrahim
Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma wanda ya yiwa jam’iyyar PDP takarar shugaban kasa a zaben shekara ta 2023 Alhaji Atiku Abubakar, ya kalubalanci abubunwan da hukumomin man fetur a Nigeria suke yiwa matatar mai mafi girma a Africa ta Ɗangote.
” Waɗannan abubunwa da suke faruwa na zagon kasa akan wannan matatar mai zai yiwa ƙasar nan illa sosai, domin zai hana masu saka hannun jari yan kasashen shigowa Nigeria domin zuba hannun jarinsu”.
Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ya fitar ranar laraba.

” Wannan matatar man ita ce mafi girma harkar Kasuwanci ta wani mutum guda ya yi, don haka bai dace ga gwamnati ta rika yi masa zagon kasa ba, saboda yadda za ta taimaka wajen bunkasa tattalin arzikin Nigeria”. Inji Atiku Abubakar
Hukumar EFCC ta kama mutum huɗu da almundahanar kuɗi a Kano
Atiku Abubakar ya kara da cewa wannan abun da ake yiwa Ɗangote a matsayinsa na dan kasa, ta yaya wanda ba dan kasar ba, zai zo ya sanya hannun jarinsa a kasar ?.
” Babu shakka a matsayin Ɗangote na dan kasar nan, baiwa Kasuwancinsa kariya zai jawo hankalin masu saka hannun jari na kasashen waje su shigo don yin Kasuwanci domin sun san ba za a yi kokarin karya su ba”.
Ya ce Kasuwancin da ya shafi harkokin man fetur da Gas suna da muhimmancin da idan Dan Kasuwa ya ce zai yi shi, gwamnati ta bashi kulawa ta musamman saboda muhimmancinta.