Daga Maryam Muhammad Ibrahim
Sanatan Kano ta kudu a zauren majalisar Dattawan Nigeria, Sulaiman Abdurrahman Kawu Sumaila ya ce shi ba dan wata Kungiya ba ne, kawai abun da ya sani shi dan siyasa ne.
” Yau Shekaru 33 ban taba cire kafa ta daga harkar siyasa ba, don haka idan anyi min adawa bata damuna, domin nima na taba zama a matsayin dan adawa”.
Kadaura24 ta rawaito Kawu Sumaila ya bayyana hakan cikin yayin da yake martani ga masu ganin baikensa saboda ya gabatar da kudirin.

“Ita Kwankwasiyya kungiya ce a cikin siyasa kuma nima Ina da kungiyar waraka, kungiyar da bana cikin ita ce irin kungiyar cigaban gari ko cigaban jiha ko kuma ci gaban wani to duk bana wannan kawai dan siyasa ne ni”. Kawu Sumaila
Sanata Kawu Sumaila ya gabatar da kudirin kirkirar sabuwar jiha daga Kano
Ya ce jagoran Kwankwasiyya ya san abun da mutanen kano ta kudu suke so shi yasa lokacin zabe ya bashi goyon baya saboda yasan cewa al’ummar kano ta kadu shi suke so shi yasa kuma suka zabe shi.
Rusau: Gwamnatin Kano Ta Bayyana Matsayarta Kan Gine-Ginen Dake Hanyar BUK
An tambaye shi cewa, shin wannan kalaman nasa an ya basa nufin fito-na-fito da tsarin Kwankwasiyya ? , kawu Sumaila ya ce Sam ba haka ba ne.
A cikin hira da Manema labarai Kawu Sumaila ya ce ya gabatar da kudirin kirkirar sabuwar jiha ta Tiga ne don cigaban al’ummar da yake wakilta kuma ba ya nadamar abun da yayi.