Yadda Sarki Aminu da Yan Sanda suka kwace ni a hannu wasu matasa – Dan majalisar NNPP

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

 

Wasu gungun matasa sun yi wa dan majalisar dokokin jihar Kano Abdul-Majid Umar dukan tsiya a wani taron da Sarkin Kano na 15, Aminu Ado-Bayero ya halarta a ranar Asabar.

Umar dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Gwale, wasu Matasa ‘yan mazabarsa ne suka kai masa hari a unguwar Goron Dutse.

Dan majalisar a ranar Litinin din nan ya ce sarki Aminu Ado Bayero da ‘yan sanda sune suka kwace shi daga hannun matasan.

Idan za a iya tunawa kadaura24 ta rawaito Aminu Ado-Bayero, a ranar Asabar din da ta gabata, ya halarci taron addu’o’i na shekara-shekara da ake yiwa kasa da kano domin neman zaman lafiya da kwanciyar hankali , wanda shugabannin darikar Tijjaniyya suka shirya a gidan Marigayi Sheikh Isyaku Rabiu da ke Goron Dutse, a karamar hukumar Gwale ta jihar.

Talla

Umar wanda ya zauna a gefen sarkin a wajen taron, amma matasan sun far masa ne jim kadan da barin wurin taron.

Kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito, matasan sun zarge shi ne da goyon bayan kudirin tsige sarkin.

Ni Dan Siyasa Ne Ba Dan Kungiya ba – Sanata Kawu Sumaila

Rahotanni sun ce matasan sun raunata dan majalisar ne kafin ya tsere cikin motar ‘yan sanda da ke wajen taron.

Dan majalisar ya shaida wa sashen Hausa na BBC a ranar Litinin cewa, dubban magoya bayan sarkin ne suka kai masa hari bayan ya bar taron ba tare da sanin ya kamata ba.

 

Umar ya ce ya bar wurin ne a lokacin da ya lura da cewa wurin babu tsaro.

“Bayan da hambararren sarkin ya isa wurin taron, sai magoya bayansa suka fara zagina da abokan aikina, suna zargin mu da soke dokar majalisar masarautun 2019 da ta kai ga tsige Sarkin.

Rusau: Gwamnatin Kano Ta Bayyana Matsayarta Kan Gine-Ginen Dake Hanyar BUK

“Sarkin da aka tube ya tare wani daga cikin fadawansa da ya yi yunkurin buge ni. Sarkin da kansa ya yi amfani da hannunsa wajen tare dukan da bafaden ya kawo, ya kuma yi wa wani wanda ya sake yunkurin duka na tsawa,” in ji Mista Umar.

Umar ya ce ya yanke shawarar barin taron ne lokacin da ya lura cewa shi kadai ne jami’in gwamnati a wajen taron.

“Na kara shiga damuwa bayan na bar wurin taron yayin da mutane dauke da muggan makamai suka far min. Na yi sauri na shiga motar ‘yan sanda. Da haka aka kubutar da ni daga harin.

“Magoya bayana biyu sun jikkata lokacin da muke kokarin barin wurin taron”, in ji dan majalisar.

Sai dai daya daga cikin hadiman sarkin kan harkokin kafafen yada labarai, Khalid Uba Adamu ya musanta cewa matasan suna cikin tawagar sarkin.

Ya ce Sarki Aminu Ado Bayero ya isa wurin taron ne da dimbin magoya bayansa, amma babu daya daga cikinsu da ke dauke da makami.

Rikicin masarautar Kano ya fara ne bayan da ‘yan majalisar a ranar 23 ga Mayu, 2024 suka soke dokar majalisar masarautun jihar ta 2019, wadda tsohon Gwamna Abdullahi Ganduje ya kirkiro sabbin masarautu hudu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi: Tinubu ya Iso Kano domin ta’aziyyar Dantata

Shugaban Nigeria Bola Ahmad Tinubu ya iso jihar Kano...

ALGON ta Kano Sa’adatu Soja ta sami sabon matsayi a kungiyar ALGON ta Ƙasa

Daga: Aliyu Danbala Gwarzo. Shugabar karamar hukumar Tudunwada kuma ALGON...

Da dumi-dumi: Tinubu zai zo Kano

Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu zai zo Kano ranar...

Tinubu ya sauya sunan jami’ar Maiduguri zuwa Sunan Muhd Buhari

Shugaba Bola Tinubu ya sauya sunan Jami'ar Maiduguri zuwa...