Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Jami’an hukumar tsaro ta farin kaya DSS sun kashe daya daga cikin wadanda suka yi garkuwa da mahaifiyar fitaccen mawakin Hausa, Dauda Kahutu Rarara, yayin da aka ce an kama guda bayan an harbe shi da bindiga.
Majiyar DSS a Kano ta ce jami’an sun kai farmakin ne maboyar masu garkuwa da mutane a cikin dajin Makarfi da ke jihar Kaduna, da sanyin safiyar Juma’a, inda suka yi musu ba-zata a lokacin da suke raba kudin fansa da suka karba.
A cewar majiyar: “Jami’an sun yi nasarar fatattakar masu garkuwar, inda nan take suka kashe daya sannan suka kama wani da ke karbar magani sakamakon harbinsa da bindiga da aka yi, yayin da aka kwato Naira miliyan 26.5 da aka biya su a matsayin kudin fansar mahaifiyar mawakin.”
Ya ce an kai harin ne bayan da aka samu bayanan sirri cewa masu garkuwar suna dajin Makarfi.
Gwamnan kano ya bayyana dalilinsa na kin dawo da Sarkin Bichi
Ya ce: “aikin ya yi nasara sosai har dayan mai garkuwa da mutane da ke karbar magani yana taimaka wa jami’an da wasu sahihin bayanai kan yadda suka yi garkuwa da ‘yan Najeriya da ba su ji ba ba su gani ba.”
Ya kara da cewa: “A gaskiya ba zan iya tabbatar muku cewa masu garkuwa da mutane Hamisu da Bature Fulani ne ba. Amma dai wanda ke karbar magani, Bature, yana taimaka wa jami’an da bayanan ayyukansu.”