Yadda DSS su ka kashe tare da kama wadanda suka sace mahaifiyar Rarara

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

Jami’an hukumar tsaro ta farin kaya DSS sun kashe daya daga cikin wadanda suka yi garkuwa da mahaifiyar fitaccen mawakin Hausa, Dauda Kahutu Rarara, yayin da aka ce an kama guda bayan an harbe shi da bindiga.

Majiyar DSS a Kano ta ce jami’an sun kai farmakin ne maboyar masu garkuwa da mutane a cikin dajin Makarfi da ke jihar Kaduna, da sanyin safiyar Juma’a, inda suka yi musu ba-zata a lokacin da suke raba kudin fansa da suka karba.

A cewar majiyar: “Jami’an sun yi nasarar fatattakar masu garkuwar, inda nan take suka kashe daya sannan suka kama wani da ke karbar magani sakamakon harbinsa da bindiga da aka yi, yayin da aka kwato Naira miliyan 26.5 da aka biya su a matsayin kudin fansar mahaifiyar mawakin.”

Talla

Ya ce an kai harin ne bayan da aka samu bayanan sirri cewa masu garkuwar suna dajin Makarfi.

Gwamnan kano ya bayyana dalilinsa na kin dawo da Sarkin Bichi

Ya ce: “aikin ya yi nasara sosai har dayan mai garkuwa da mutane da ke karbar magani yana taimaka wa jami’an da wasu sahihin bayanai kan yadda suka yi garkuwa da ‘yan Najeriya da ba su ji ba ba su gani ba.”

Ya kara da cewa: “A gaskiya ba zan iya tabbatar muku cewa masu garkuwa da mutane Hamisu da Bature Fulani ne ba. Amma dai wanda ke karbar magani, Bature, yana taimaka wa jami’an da bayanan ayyukansu.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Ku ba da gudunmawa kano ta zauna Lafiya – Waiya ya shawarci yan jaridun yanar gizo

Gwamnatin jihar Kano ta bukaci kafafen yada labarai na...

KAROTA ta tabbatar da aniyarta na inganta matsayin jami’anta

Hukumar Kula da Zirga-zirgar Ababen Hawa ta Jihar Kano...

Sarkin Sanusi ya amince da nadin sabon mai unguwar Hotoro GRA

  Mai martaba Sarkin Kano na 16, Malam Muhammadu Sanusi...