Gwamnan kano ya bayyana dalilinsa na kin dawo da Sarkin Bichi

Date:

Daga Samira Ahmad

Gwamnan jihar kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya ce girma da darajar Bichi a masarautar kano ta sa tasa bai dawo da Sarkin Bichi ba.

Idan za a iya tunawa kadaura24 ta rawaito a Kwanakin baya gwamnatin jihar kano ta rushe sabbin masarautu da Ganduje ya samar a shekara ta 2019, bayan rushe dokar masarautun da majalisar dokokin jihar kano ta yi.

” Ita Bichi tana da muhimmanci sosai ga masarautar kano , saboda muhimmancinta ba konne mutum ake kaiwa ya zama hakimi ba, dole sai dan sarki don haka ba mu dawo da ita ba muka bar ta yadda tarihi ya nuna”.

Talla

Abba Kabir Yusuf ya bayyana hakan ne yayin wani taro na masu ruwa da tsakin jam’iyyar NNPP na kano a gidan gwamnatin jihar.

Ba haka mu ka tsammata daga gareku ba – Atiku Abubakar ga majalisar wakilai

Ya a baya dan sarkin kano shi ake nadawa a matsayin hakimin Bichi hakan tasa bayan rusa masarautun suka bar da a matsayin da take da shi tun asali.

Yayi fatan Sarki Sanusi II zai tura mutum mai kima da zai rike kasar Bichin a matsayin hakimi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Tinubu ya bijiro da harajin da zai sa farashin man fetur ya karu

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da ƙaddamar...

Sabbin Nau’o’in cutar Shan Inna 4 sun bulla a Kano

Hukumar kula da lafiya a matakin farko ta jihar...

NDLEA ‘Yan Sanda da Gwamnatin Kebbi Sun Karyata Jita-jitar Samar da Filin Jirgin Sama na Boye a jihar

  Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta...

Kotu a Kano ta kawo karshen Shari’ar wata Tunkiya

Daga Dantala Uba Nuhu, Kura An kawo ƙarshen shari’ar wata...