Daga Zakaria Adam Jigirya
Ɗan Majalisa mai wakiltar mazaɓar kananan hukumomin Kiru/Bebeji a jihar Kano, Hon Abdulmumin Jibrin Kofa, a ranar Lahadi ya shirya taron addu’a na musamman a gidansa da ke Kofa, Bebeji, inda ɗaruruwan malamai suka yi wa mazabarsa da Kano da ma Najeriya addu’a.
Daga bisani kuma ɗan majalisar ya shirya babban taron motsa jam’iyya wanda dubban magoya baya suka halarta, inda ya jinjina musu kan jajircewarsu da goyon bayan da suke bayarwa.
Hon. Kofa ya ba su tabbacin cewa ba zai yi ƙasa a gwiwa ba wajen ci gaba da bayar da tallafin da kuma ayyukan raya ƙasa da yake yi daga yi daga aljihunsa da kuma na gwamnatin tarayya .
Da dumi-dumi: Tinubu ya baiwa tsohon Sanatan Kano ta tsakiya mukami
Daga cikin waɗanda suka halarci taron akwai Shugaban jam’iyyar NNPP na Kano, Hashimu Sulaiman Dungurawa da ’Yan Majalisar jiha na mazabar Kiru (Abubakar Tasi’u Rabula) da na Babeji (Ali Mohammed Tiga), Shugaban Ma’aikatan Jihar Kano, Abdullahi Musa da kuma dattawa (Alhaji Jibrin Dan-Ako da Alhaji Dankaka Hussaini Bebeji) da
Sani Ibrahim Paki
Hadimin ɗan majalisar kan yaɗa labarai
14-07-2024
Ga hotunan yadda aka gudanar da taron: