Cibiyar musulunci mai zurfafa bincike akan ilimi ta kasa ( IIIT) ta bukaci yan jaridu da su rika kaucewa duk wani labarai da zai cutar da Musulunci ta kowacce fuska.
Shugaban Cibiyar ta IIIT Dr. Sa’idu Ahmad Dukawa ne ya bayyana hakan lokacin da Cibiyar da hadin gwiwar cibiyar yan jaridu ta kasa reshen jihar kano NUJ suka shirya bitar yini guda ga yan jaridu a Kano.
” Mun shirya wannan bitar ne domin mu tunatar da yan jaridu muhimmanci aikin su da kuma yadda za su kiyaye ka’idojin aikin wadanda dama tuni Alqur’ani mai girma yayi bayani akan wasunsu”.
Dr. Sa’idu Ahmad Dukawa wanda guda cikin daraktocin cibiyar Mustapha Ibrahim Cinade ya wakilta ya ce akwai bukatar yan jaridu su rika tsayawa akan gaskiya da yin Adalci a cikin labaransu.
” A wannan cibiyar muna gudanar da aiyukan da suka shafi yada Addinin Musulunci, rubuce-rubuce wayar da kan al’umma da musuluntar da Ilimi don yayi daidai da koyarwar addinin Musulunci”. A cewar sa
Yanzu-yanzu: Tinubu ya baiwa Baffa Babban Dan’agundi Mukami
Ya kuma yi kira ga yan jaridu da su tabbatar suna bin ka’idojin aikin jarida wadanda suke yi daidai da koyarwar addinin Musulunci.
Da yake jawabi a wurin taron shugaban kungiyar yan jaridu ta kasa reshen jihar kano Kwamaret Abbas Ibrahim ya ba da tabbacin bitar za ta taimaka wajen kara inganta harkokin aikin jarida.
” Na yi farin ciki da muka yi wannan hadin gwiwar da cibiyar IIIT saboda na yi imanin za ta haifar da ‘Da-mai ido musamman ga yan jaridarmu masu tasowa”. A cewar Abba
Ya bukaci mahalarta taron da su yi amfani da abun da suka koya wajen inganta aiyukan su na yada labarai .
A makalar da ya gabatar mai taken “Ka’idojin aikin jarida a mahangar Addinin Musulunci” Dr. Ibrahim Suraj ya hori yan jarida da su rika gudanar da aikinsu akan doron Addinin Musulunci, tare da bin ka’idojin aikin don inganta aikin nasu.
” Ku guji yin karya da rashin Adalci a labaranku, domin yin su yana bata aikin bayan kuma aikin na ku yana da asali a Musulunci domin akwai ayoyi daga al’qur’ani mai girma da hadisan Annabi Muhammad amincin Allah ya tabbata a gare shi, sun yi Bayanin yadda ya kamata ku gudanar da wannan aikin” . A cewar Dr. Ibrahim Suraj