Daga Aliyu Danbala Gwarzo
Shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da nadin Sanata Bashir Garba Lado a matsayin mai baiwa shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin majalisar dattawa .
Mai baiwa shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai Ajuri Ngelale ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya sanyawa hannu a ranar Asabar.
Shugaban ya bayyana Lado Mohammed a matsayin gogaggen dan siyasa kuma dan kasuwa daga jihar Kano.
Iftila’i: Gobara ta tashi a masarautar Kano
Muhammad Bashir Garba Lado tsohon Sanata ne da ya wakilci Kano ta tsakiya kuma tsohon Darakta-Janar na hukumar kula da yan gudun hijira ta kasa.
Yanzu-yanzu: Tinubu ya baiwa Baffa Babban Dan’agundi Mukami
Ngelale ya ce Shugaba Tinubu “yana tsammanin sabon mai ba shi shawara na musamman kan harkokin majalisar dattawa zai yi amfani da kwarewarsa wajen inganta alakar dake tsakanin bangaren zartarwa da majalisa dattawa.”