Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa
A yau ne ake sa ran kotun koli za ta yanke hukunci kan karar da gwamnatin tarayya ta shigar a kan gwamnonin jihohi 36, Inda ta ke neman kotun ta tilastawa gwamnonin baiwa kananan hukumomi 774 na kasar nan yancin cin gashin kansu.
Kotun kolin ta sanar da dukkan bangarorin da ke kara ta hannun lauyoyinsu cewa a yau zata yanke hukuncin .

Kotun kolin dai a ranar 13 ga watan Yuni ta dage yanke hukunci kan karar da ake zargin gwamnatocin jihohi. A zaman da aka yi na karshe, tawagar alƙalai bakwai karkashin jagorancin Mai Shari’a Garba Lawal, ya bayyana cewa a shirye suke da za su yanke hukunci bayan sauraron bahasi daga gwamnonin jihohin kasar nan 36, wadanda manyan lauyoyinsu suka wakilce su.
Rikicin Masarautun Kano: Yadda Matasa suka hana wakilin Sarki Sanusi shiga gidan sarkin Rano
Jihohin dai sun yi zargin cewa Lateef Fagbemi, babban lauyan gwamnatin tarayya kuma ministan shari’a ba shi da hurumin fara daukar matakin a madadin gwamnatin tarayya.