Daga Zakariyya Adam Jigirya
Shugaban kamfanin takin zamani na Boko fertilizer Alhaji Naziru Abdullahi Al-hassan ya bayyana cewa Babban kalubalen da masu kamfanonin taki suke fuskanta a Nigeria shi ne kwaiwayon kayansu da wasu bata gari suke yi.
” Yin taki na jabu shi ne kaso 70 cikin 100 na matsalolin da muke fuskanta, ba wai takin zamani na Boko fertilizer kadai ba har da sauran kamfanin takin, Amma cikin ikon Allah kungiyarmu ta masu kamfanonin yin takin zamani ta na nan tana aiki ba dare ba rana domin daukar matakan da suka dace”.
Alhaji Naziru Abdullahi ya bayyana hakan ne lokacin da yake zantawa da wakilin jaridar kadaura24 a Kano.
Ya ce su a matsayin su na kamfanin takin zamani da gwamnati ta sahalle musu gudanar da wannan Kasuwanci, suna iya bakin kokarinsu don ganin sun inganta kayansu, Kuma yace manoma ma shaida ne akan ingancin takin zamani na Boko fertilizer.
” Saboda ingancin takin mu na Boko fertilizer manoma da yan kasuwar taki daban-daban a Nigeria suna kiranmu ko su aiko mana da sakon godiya bisa yadda muke inganta takin zamani mu na Boko fertilizer”. Inji Naziru Abdullahi Al-hassan
Da yake tsokaci kan abun da ya faru a jihar Katsina game da takin da gwamnatin jihar ta rabawa manoma, Alhaji Naziru Abdullahi Al-hassan ya ba da tabbacin takin da ake kuka da shi ba na kamfanin Boko fertilizer ba ne.
” Mun Kai takin zamani na Boko fertilizer sama da dubi 80 jihar Katsina, amma abun mamaki sai aka ce an sami wasu kusan dubu biyu da na jabu, wanda hakan ya tabbatar mana cewa wancan na jabun ba namu bane, wasu marasa kishi ne suka gauraya da namu don biyan bukatar kansu”. A cewar shi
” A Shekarar da ta wuce gwamnatin jihar Zamfara ta sayi takin mu na Boko fertilizer ba ta sami wata matsala ba, haka gwamnatin jihar kano ita ma bata sami matsala ba, haka wani dan majalisa daga Borno shi ma ya sayi takin mu na Boko fertilizer kuma shi ma bai sami matsala ba, to ya za a ce Mun kai taki marar kyau Katsina, tabbatas hakan ba zai yiwuwa ba”.
Alhaji Naziru Abdullahi Al-hassan ya bukaci gwamnatin jihar ta Katsina da ta zurfafa bincike domin gano inda matsalar ta fito, Inda ya ba da tabbacin takin su mai inganci ne kuma ba su da wata tantama akan sa.
Ya kuma ba da tabbacin kamfanin takin zamani na Boko fertilizer zai cigaba da inganta kayansa kamar yadda aka sani, don inganta harkokin noma a Nigeria.