Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa
Rundunar yan sintiri dake karamar hukumar gezawa ta yabawa masu ruwa datsaki na karamar hukumar bisa yadda suke tallafawa harkar tsaron yanki.
kwamandan rundunar Bello Abdulrahaman Gunduwawa ne ya bayyana hakan yayin wata ganawa da jaridar kadaura24.
Ya bayyana cewa sun fito da sabon salon na yakar masu aikata laifuka, wanda hakan ya sa suka sami nasarorin kama masu laifi a yankin karamar hukumar gezawa.

Kwamandan ya kara dacewa wannan nasarori da suke samu sun samune tahanyar Addu’o’in da malaman yanki ke yi musu da kuma tallafin da suke samu daga jagororin yakin nasu da kuma irin bayanan siri da al’ummmar karamar hukumar ta gezawa suke ba su.
Karin haske kan matakin gwamnatin tarayya na dakatar da kuɗin harajin kayan abinchi
Ya yabawa sauran jami’an tsaron yanki kan irin goyon bayan da suke basu a koda yaushe ya kuma bukaci da suci gaba da zage damtse kar su gajiya wajan gudanar da aikisu.
Daga karshe yayabawa shugaban su na jahar kano baki daya bisa irin gudunmawar da ya ke ba su.