Karin haske kan matakin gwamnatin tarayya na dakatar da kuɗin harajin kayan abinchi

Date:

Gwamnatin Tarayya ta amince da shigo da muhimman kayan abinci kamar su shinkafa, wake, alkama da masara ba tare da biyan kuɗin haraji ba, domin rage tasirin tsadar kayan abinci a Nigeria.

Ministan Noma da Samar da Abinci, Sanata Abubakar Kyari ne, ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a Abuja.

Ya ce shugaba Tinubu ya amince da janye ƙudin fito kan muhimman kayan abincin ne har tsawon kwanaki 150, domin sauƙaƙa tsadar kayayyakin abinci da ake fama da su.

Wannan wani ɓangare ne na tsare-tsaren shugaban ƙasa da nufin daidaita tattalin arziƙi da samar da abinci a faɗin ƙasar nan.

Talla

Ministan, ya bayyana irin ƙoƙarin da Gwamnatin Tarayya ke yi na yaƙi da hauhawar farashin kayan abinci.

Tsada da matsin rayuwa ya ƙaru tun bayan da Shugaba Tinubu ya hau kan karagar mulki a ranar 29 ga watan Mayun 2023.

Rikicin Sarautar Kano: Tinubu ya mayar da martani kan zargin shugaban NNPP

Gwamnati za ta shigo da alkama da masara daga waje

Sanarwar ta ce baya ga janye ƙuɗin fito ga ’yan kasuwa masu buƙatar shigo da kayan abinci.

Har wa yau, Gwamnatin Tarayya za ta shigo da alkama kimanin tan dubu 250 da masara tan 250 da za ta bai wa kamfanoni jihohi da ke sarrafa su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin gida: Jam’iyyar APC ta Fara Tuhumar Kakakinta na Kano Ahmad S Aruwa

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jam'iyyar APC ta Mazabar Daurawa a...

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...