Dan majalisar Nasarawa ya tasamma warware matsalar asibiti a wasu unguwannin yankin

Date:

Daga Rabi’u Usman

 

Al’ummar unguwannin Hotoro yandodo, Hotoron Arewa, Hotoron ladanai, layin mai allo da Jar kuka da kuma walalambe duk a cikin karamar hukumar Nassarawa a kano, sun jima suna koke akan matsalar da suke fama da ita na ababen more rayuwa shekara da shekaru, kama daga kan matsalar Hanya, ruwan Sha, makaranta, makabarta, asibiti kuma an rasa Wanda zai kawo musu dauki.

Sai dai a wannan karon za’a iya cewa kayan su ya tsinke a gindin kaba, inda wadannan mutanen yau bakin su har kunne domin murna da farin cikin abinda suka samu.

Al’ummar unguwar Hotoron Arewa ta bakin Dagacin su Alhaji Yahaya Yakubu Hotoro, sun yabawa kokarin Dan majalisar tarayya Mai wakiltar karamar hukumar Nassarawa bisa yadda ya kawo musu dauki domin magance musu matsalar Asibitin da suke fama dashi sama da shekaru 50 da suka gabata.

Asibitin Best Choice Zai Kaddamar Da Fara Ayyukan Kula Da Hakora Kyauta

Wanda yanzu haka dai an fara Gina wani katafaren asibiti a wannan yanki domin magance matsalar yawan haihuwa barkatai a kan hanyar zuwa asibiti Mai nisa daga wadannan unguwanni.

Yahaya ya ce matukar zaba rika yin irin wannan Siyasar ta samar da ayyukan raya kasa ba tare da cin mutunci kuma ba tare da ta’addanci ba la shakka za’a samar da ingantaccen shugabanni a tsakanin Al’umma.

Talla

Daga nan ya Mika sakon godiyar su ga Hassan Hussaini Wanda ya samar musu da wannan gagarumin aikin asibiti Wanda ake sa rai za’a kammala shi nan da watanni uku masu zuwa.

A nasa bangaren wakilin Dan majalisar tarayya mai wakiltar karamar hukumar Nassarawa Hassan Hussaini Wanda ya samu wakilcin guda daga cikin wakilan sa a mazabar Hotoron Arewa Hon Shamsu Galadi ya nanata kudirin Dan majalisar na samar musu da makaranta a yankin Mai dauke da aji guda shida na bene nan da makonni biyu masu zuwa.

Ya kara da cewar, Dan majalisar yayi kira ga Al’ummar wannan yanki dasu kasance masu taimakawa juna da Addu’oi na musamman wajen samun nasarar aikin da ake yi.

A karshe wasu daga cikin mutanen unguwa, musamman kungiyar samar da cigaban unguwannin Hotoron Haye, Hotoron Arewa, Hotoron ladanai da Kuma yandodo sun Mika sakon godiyar su ga Dan majalisar tarayya Mai wakiltar karamar hukumar Nassarawa Hon Hassan Hussaini tare da yin kira ga gwamnan kano ya kawo musu dauki na matsalar hanyar da suke fama da ita.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Wata sabuwa: Sanata Barau Jibrin ya gana da Baffa Bichi da Muhd Diggol

Tsohon sakataren gwamnatin Jihar Kano Dakta Abdullahi Baffa Bichi...

Rikicin Masarautar Kano: Kotu ta Sake Sabon Hukunci

A wani sabon yanayi na rikicin Masarautar Kano, Kotun...

Gidauniyar Aliko Dangote za ta rabawa ‘yan Najeriya miliyan daya shinkafa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Gidauniyar Aliko Dangote ta raba buhunan...

Rufe Makarantu da azumi: Ministan Ilimi ba ta da ilimin harkokin mulki – Jafar Sani Bello

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Tsohon dan takarar gwamnan jihar Kano...