Daga Halima Musa Sabaru
A wani bangare na bikin kaddamar da sabon sashin kula da hakora, asibitin kwararru na Best Choice ya kaddamar da shirin kula da hakora kyauta na tsawon sati 2 a Ofishinsa dake Tal’udu a birnin Kano.
Shugaban Asibitin Auwal Lawan ne ya bayyana hakan a lokacin da yake ganawa da manema labarai a mutsugunun asibitin na dindindin dake kan titin Aminu kano.
Lawan ya jaddada cewa, sabon sashin kula da hakoran zai duba mara sa lafiya tare da ba su shawarwari kyauta, gyaran hakora da aikin goge hakora kyauta na tsawon makonni biyu.
Daga nan Auwal ya jaddada bukatar dake akwai ga duk wadanda ke fama da matsalolin hakora cewa, asibitin yayi tanadin abubuwan da suka dace game da ƙwararrun likitocin haƙora da suka goge tsawon shekaru, da kuma isassun kayan aikin haƙora na zamani, tsarin kula da marasa lafiya duk a kyauta na tsawon mako biyu.
Ya jaddada kudirinsu na share hawayen marasa lafiya inda ya bukace su da kada su yi sanya wajan cin gajiyar wannan tagomashi na kulada lafiyar baki da ta hakori.

Idan za a iya tunawa, asibitin ya koma babbar helkwatarsa ta dindindin dake shatale-talen Tal’udu kusa da Kwalejin Bashir El-rayya, dake kan titin Aminu Kano anan birnin Dabo.
Ya kara da cewar baya ga ficen da suka yi a fannin kula da mafitsara, asibitin na aiwatar da muhimman ayyukan da suka hada da jinyar kananan yara (Paediatrics), tiyata (surgery), kula da masu tabin hanka( psychiatry), bangaren hakora (Dentals), gashin kashi ( physiotherapy) sashin kula da cutukan mata (Gynaecology) da bangaren masu kula da masu ciki da haihuwa, bangaren fata (dermatology), manyan dakin gwaje-gwaje, kantin magani, da sashin kula da jarirai.
Lawan ya tabbatar da cewa asibitin cike yake da na’urorin kiwon lafiya na zamani irin na kasashen duniya, ga kuma tsayayyiyar wutar lantarki 24-7.