Babban Limamin Masallatan Harami Sheikh Abdurrahman Sudais ya sanar cewa za a fassara hudubar Ranar Arafa kai-tsaye a cikin harshen Hausa da wasu harsuna 19 domin karuwar alhazai da sauran al’ummar Musulmi a fadin duniya.
Hajjin bana: Yau wa’adin shigar Maniyata ƙasar saudiyya ke cika
Sheikh Sudais ya ce ana sa ran sama mutum miliyan 100 za su saurari hudubar wadda Sheikh Maher Al Mu’ayqaly zai gabatar a Masallacin Namirah ta kafofin watsa labarai daban-daban.
Za dai a gudanar da tsaiwar Arafat ne a ranar asabar 08 ga watan zul-hijja, Inda aka sa ran dukkanin wadanda suka je aikin hajji su isa filin na Arfa domin tsayiwar na daga cikin rukunan aikin hajji .