Daga Rukayya Abdullahi Maida
Hukumar karbar korafe-korafe da Yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano ta ce ta fara gudanar da bincike kan badakalar kudaden da gwamna Abba Yusuf ya baiwa masu sana’ar sayar da kaya a danjojin jihar kano, a matsayin tallafi .
Shugaban Hukumar Muhuyi Rimin-Gado, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN a ranar Lahadi a Kano cewa hukumar na gudanar da bincike don gano tare da gurfanar da wadanda ke da hannu a gaban kuliya.
Hukumar na binciken lamarin kuma duk wanda aka samu da hannu za a gurfanar da shi gaban kotu.
“Hukumar ta kuduri aniyar hana cin hanci da rashawa da yaki da masu tauye hakkin wadanda gwamnatin jihar kano ta tallafawa,” Rimin Gado ya shaida wa NAN.
Kwankwaso ya bayyana wadanda suka hana gwamnan Kano sakat tsawon Shekara Daya
Binciken ya biyo bayan wani faifan bidiyo da ya nuna inda ake zargin wasu jami’ai sun tursasa wadanda suka amfana da tallafin su mika wani kaso mai tsoka na tallafin Naira 50,000 da kowannen su ya samu yayin bikin raba tallafin kudaden da gwamnatin jihar kano ta yi.
NAN ta ruwaito cewa a kwanakin baya gwamnan jihar kano Abba Kabir Yusuf ya baiwa masu sana’a a kan tituna su kimanin 465 Naira 50,000 kowannensu domin bunkasa sana’arsu.
Jaruma Hadiza Gabon ta baiwa mata masu sha’awar shiga Kannywood shawara
Sai dai a wani faifan bidiyo mai tsawon dakika 60, daya daga cikin wadanda suka ci gajiyar tallafin mai suna Malam Nura Isa ya yi zargin cewa wasu daga cikin jami’an gwamnati ne suka tilasta masa ya mayar da Naira 45,000 daga cikin tsabar kudi na Naira dubu N50,000 da aka ba shi.
Isa ya yi zargin cewa yana cikin mutane100 da jami’ai suka tilasta musu don karbar kuɗin a wajen su.
An kuma tattaro cewa akasarin wadanda aka zaba domin cin gajiyar shirin an hana su shiga wurin da aka gudanar da taron yayin da aka mika kudaden ga ‘yan bogi.