Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Hukumomi a ƙasar saudiyya sun tabbatar da ganin jinjirin watan Zul Hijja a wannan ranar ta alhamis.
Kadaura24 ta rawaito Sanarwar da shafin Haramain Sharifain ya fitar ta ce gobe Juma’a ita ce ranar 01 ga watan zul-hujja 1445.
Rikicin Sarautar Kano: Kotu Ta Sanya Ranar Yanke Hukunci
Sanarwar ta ce za a gudanar da tsaiwar Arafat a ranar asabar 15 ga watan yuni 2024. Yayin da za a gudanar da idin Sallah babba a ranar lahadi 16 ga watan yuni 2024.