Daga Rahama Umar Kwaru
Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta bayyana cewa Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, ba zai jagoranci sallar Juma’a a babban masallacin Kano ba kamar yadda ake ta yadawa.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Usaini Gumel wanda ya bayyana hakan, ya ce Aminu Ado Bayero zai yi Sallar Juma’a a masallacin da ke cikin fadar Nasarawa, inda yake zaune a halin yanzu.
Gumel ya kara da cewa ana sa ran shi kuma Sarkin Kano na 16, Muhammad Sanusi II zai jagoranci sallar Juma’a a babban masallacin Juma’a na cikin gari.
Fargaba a Kano: Sarki Sanusi da Sarki Aminu na shirin gabatar da Sallar Juma’a a Masallacin Guda
Kadaura24 ta ga sanawar da hadiman Sarki Aminu Ado Bayero suka rika sanya wa tun a jiya cewa suna gayyatar masoya sarki da su fito domin raka shi zuwa sallah Juma’a a masallacin cikin garin kano.
Sai dai kwamishinan ‘yan sandan ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Najeriya ta wayar tarho a ranar Juma’a cewa sarki Aminu ba zai gudanar da sallar Juma’a a masallacin cikin garin ba.
EFCC ta fara bincike kan zargin da Ake yiwa Kwankwaso na almundahanar wasu kudade
Ya kara da cewa ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro a jihar za su samar da ingantaccen tsaro don baiwa mazauna birnin Kano damar gudanar da sallar jam’i cikin lumana.
“’Yan sanda za su ci gaba da samar da tsaro da ya dace domin tabbatar da hakan zai baiwa mazauna yankin damar gudanar da Sallar Juma’a cikin kwanciyar hankali ba tare da barazana ga rayuka da dukiyoyin su ba,” inji shi.