Daga Samira Ahmad Ibrahim
Wasu Matasa Sun gudanar da Zanga-Zangar kin Amince da dokar da ta rushe sabbin masarautu da tsohon gwamnan kano Abdullahi Ganduje ya samar a shekara ta 2019.
Jagoran zanga-zangar Aliyu Harazimi Rano ya ce sun gudanar da zanga-zangar lumanane domin nunawa gwamnatin jihar kano da majalisar dokokin jihar kano rashin amincewar da rushe musu masarautar Rano.
Gaskiyar Lamari Kan Halin Da Ake Ciki a Masarautar Kano
” Allah ya Sani tun da muke ba mu taba ganin cigaban da muka gani a karamar hukumar Rano ba, kuma duk cigaban ya samu ne sakamakon masarautar mu da aka dawo mana da ita”. Inji Aliyu Harami
Yace rushe masarautar rano da aka yi zai haifar musu da koma baya ta fannoni daban-daban na rayuwar al’ummar yakin.
Jami’an Tsaro Sun Bayyana Matsayarsa kan Dambarwar Masarautar Kano
” Albarkacin masarautar rano an gina mana asibitin mai gado 400 sannan an yi mana Hanyoyin manya da kanana, kai Mun sami cigaban da ba zamu iya fada ba bayyanawa ba”. A cewar Harazimi Rano
Yace ya kamata mutanen jihar kano su sani masarautar rano ba kirkirarta akai ba , dama tana nan kawai gwamnatin da ta gabata ta dawo da martabar masarautar ne.