Daga Rukayya Abdullahi Maida
Alhaji Aminu Ado Bayero, Sarkin Kano na 15, ya shigo jihar Kano da asubahin wannan rana ta asabar, inda yanzu haka yake gidan Sarkin Kano na Nasarawa dake kan titin gidan gwamnatin kano.
Jaridar kadaura24 ta jiyo tun a jiya da daddare masoyan sarki Aminu suna bada sanarwar zai shigo kano yau (asabar) don haka aje a taro shi da karfe 8 na safe a filin jirgin sama na malam Aminu kano.
Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito Gwamna Abba Kabir Yusuf wanda ya rushe Aminu Ado Bayero tare da wasu Sarakunan da magabacinsa Abdullahi Ganduje ya nada, ya ba su sa’o’i 48 da su bar fadarsu tare da mika kayan masarautun ga kwamishinan kananan hukumomi da masarautu.
Daga nan ne ya bada sanarwar maido da Alhaji Muhammadu Sanusi, wanda Ganduje ya tsige shi a shekarar 2020.
Kwankwaso ya Magantu Kan Rushe Masarautun Kano
Gwamnan ya mikawa Sanusi wasikar sake nada shi a ranar Juma’a kuma ya jagoranci sallar Juma’a a gidan gwamnati dake Kano.
Amma da sanyin safiyar Asabar, Aminu Ado Bayero ya koma Kano inda dimbin magoya bayansa suka tarbe shi.
Daga baya ya koma cikin fadar da ke Nassarawa, wanda ya haifar da rudani.
Sai dai tun cikin daren jiya Sarki Muhammadu Sanusi II ya shiga gidan dabo bisa rakiyar Gwamnan Yusuf da mataimakinsa da sauran mukarraban gwamnatin Kano.
Kotu Ta Baiwa Gwamnatin Kano Umarni Kan Rushe Sarakuna Da Dawo Da Sanusi
Idan dai zaku iya tunawa kadaura24 ta baku labarin cewa wata kotun tarayya dake zaman ta a Kano ta ba da umarnin dakatar da aiwatar da sabuwar dokar data rushe sabbin masarautun Kano har sai ta gama sauraron karar da aka kai gabanta.
Amma da sanya safiyar wannan rana ta asabar gwamnatin jihar kano ta umarci kwamishinan yan sandan jihar kano da ya kama Sarki Kano na 15 Aminu Ado Bayero saboda shigowar ka iya haidar da ruɗani a jihar.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Kano Sanusi Bature Dawakin Tofa ya aikowa kadaura24, yace gwamnan ya bada umarnin kama sarki Aminu ne kasancewarsa wanda alhakin kula da zaman lafiyar al’ummar jihar Kano ya rataya a wuyansa.
Sai dai kuma Aminu Ado Bayero ya shigo Kano ne bisa rakiyar dumbin jami’an tsaro domin gudun abun da iya faruwa.
Duka dai a safiyar asabar din nan mataimakin gwamnan kano Com. Aminu Abdussalam Gwarzo, a zantawarsa da manema labarai a gidan sarkin kano ya yi zargin cewa mai baiwa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro shi ne ya shiya dawo wa Sarki Aminun, wanda kuma ba su san dalilinsa na yin hakan ba.
Jaridar kadaura24 zata cigaba da bibiyar lamarin domin sanar da ku sahihin halin da ake ciki.