Ba ni da hannu a rikicin masarautar Kano – Nuhu Ribado

Date:

 

Ofishin mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro ya musanta zargin hannun Nuhu Ribadu a komawar da Alhaji Aminu Ado Bayero ya yi zuwa Kano.

Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta Mataimakin gwamnan jihar kano Kwared Aminu Abdussalam ne ya zargi Nuhu Ribadu da kitsa komawar Aminu Ado Bayero zuwa Kano ta hanyar ba shi jami’an tsaro da jirgin sama domin mayar da shi jihar.

”Mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro ne ya bayar da jirage guda biyu domin ɗauko tsohon sarki domin su kawo shi Kano”, in ji mataimakin gwamnan.

Gaskiyar Lamari Kan Halin Da Ake Ciki a Masarautar Kano

To sai dai kakakin Nuhu Ribadun, Zakari Mijinyawa ya shaida wa BBC cewa babu hannun mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro a komawar tsohon sarkin.

”Ba gaskiya ba ne, babu wanda ya bayar da jirgi domin mayar da shi, saboda wannan ba aikinmu ba ne”, in ji Mijinyawa.

Hotunan Yadda Sarkin Muhammad Sanusi II ya gudanar da Zaman fada a Masarautar Kano

Dangane da zargin da mataimakin gwamnan ya yi cewa har da jami’an tsaro ofishin Ribadun ya aika Kano, Zakari ya ce ba haka batun yake ba.

”Babu wani jami’in tsaro da muka tura Kano, ai suma suna da jami’an tsaro, ai kwamishinan ‘yan sandan jihar ya gabatar da taron manema labarai, kuma kowa ya ji yana cewa aikinsa yake yi, ba wanda ya saka shi”.

Ya ce bai kamata a riƙa sanya siyasa a cikin kowane irin batu ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...

Bai dace ɗalibai su rika murnar kammala karatu ta hanyoyin da ba su dace ba – Mal Ibrahim Khalil

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa ‎ ‎ ‎Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano...