Hasashen yanayin da zai kasance yau laraba a birnin Kano da wasu jihohin Nigeria

Date:

Daga Nasiba Rabi’u Yusuf

 

Hasashen masana yanayi ya nuna cewa yau laraba 22-05-2024 dai-dai da 14 ga watan Dhul-Qada 1445 bayan hijira, idan Allah ya so za’a sami zafin rana a jihar Kano wanda zai kai 42 bisa ma’aunin zafi, tare da dumamar yanayi da zai kai
47 cikin dari.

Kadaura24 ta rawaito yanayi ranar zai kasance mai zafi sosai, Inda ranar zata fara zafi sosai daga misalin karfe 12 na rana har zuwa karfe 6 na yamma Sannan yanayin ya Sauya.

Hasashen dai ya nuna cewa ranar zata fara zafi ne daga lokaci da zafin ranar ya kai 39 inda zai sauya zuwa 42 bisa ma’aunin zafi.

Da dumi-dumi: Majalisar Dokokin Kano ta Bayyana Matsayarta Kan Dokar Masarautu ta Jihar

A jihar Kano dai babu yiwuwar samun ruwan sama a yau

Jihar Kano dai na fuskantar tsananin zafi a yan Kwanakin nan, Wanda hakan yasa masana suke baiwa al’umma mazauna jihar shawarar yadda zasu kare kan su daga illar da zafin ranar ka iya yi musu.

Shawarwarin da likitoci suke bayarwa sun hadar da takaita shiga Rana, yawaita shan ruwa, sanya kaya masara nauyi da dai sauransu.

Kaduna hasashen ya nuna a jihar Kaduna zafin rana zai kai 36 bisa ma’aunin zafi.

Yadda Gwamna Yusuf Ya Siyawa ‘Yan Majalisar Dokokin Kano Motocin alfarma na N2.78bn

Abuja Kuna hasashen ya nuna zafin ranar zai kai 34 bisa ma’aunin zafi

Jihar Yobe kuma hasashen ya nuna cewa zafin rana zai kai 45 bisa ma’aunin zafi.

Jihar Kebbi ita kuwa zafin ranar zai kai 41 bisa ma’aunin zafi .

Birnin maiduguri na jihar Borno zafin ranar zai kai 44 bisa ma’aunin zafi.

ABIN LURA: Hasashen ka iya chanjawa a kowanne lokaci.

Ku biyo mu gobe don kawo muku yadda hasashen zai kasance

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin gida: Jam’iyyar APC ta Fara Tuhumar Kakakinta na Kano Ahmad S Aruwa

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jam'iyyar APC ta Mazabar Daurawa a...

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...