Hajjin Bana: Ƙasar Saudiyya Ta Samar Da Wata Lema Ta Musamman Ga Mahajjata

Date:

Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa

 

Ma’aikatar Hajji da Umrah ta kasar Saudiyya ta samar da wata lema ta musamman wacce zata baiwa mahajjata kariya daga rana, sannan su ajiye yan kananan kayiyakinsu a ciki kuma zasu iya yin sallah da ita ba tare da sun rike ta ba.

Ma’aikatar ta ce ta samar da lemer ta musamman ne domin inganta jin daɗin mahajjata.

Ga wasu daga cikin abubunwan da sabuwar lemar mahajjatan ta kunsa:

Hasashen yanayin da zai kasance yau laraba a birnin Kano da wasu jihohin Nigeria

Kariyar UV: An tsara laima don samar da kariya ga mahajjata daga zafin rana saboda tsahon lokacin da zasu kwashe suna cikin Rana a yayin Ibadar aikin hajjin.

Aljihu na Adana kaya: Kowace lema tana ɗauke da aljihun da zai baiwa alhazai damar ɗaukar abubuwan bukata na yau da kullun kamar kwalbar ruwa ko abin sallah, wanda hakan zai sauƙaƙa wa alhazai yayin da suke ibada ba sai sun tsaya neman ruwa ba.

Yadda Gwamna Yusuf Ya Siyawa ‘Yan Majalisar Dokokin Kano Motocin alfarma na N2.78bn

Ba Ta Maruki: Daya daga cikin abubuwan ban sha’awa na wannan lemar shi ne ƙirarta ta musamman ce da mahajjatan basa bukata rike ta da hannu saboda makalata ake a jikin Kai, ka ga kenan idan mahajjaci zai yi Sallah baya bukatar sai ya ajiye ta .

Hukumomin kasar Saudiyya dai na cigaba da fito da nau’o’i na fasaha saboda samar da sauki ga mahajjatan bana don samar musu da walwala yayin da suke gudanar da ibadar aikin hajjin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin gida: Jam’iyyar APC ta Fara Tuhumar Kakakinta na Kano Ahmad S Aruwa

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jam'iyyar APC ta Mazabar Daurawa a...

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...