Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya bukaci kasar ta Netherland ta baiwa jihar goyon bayan diflomasiyya domin habaka harkokin noma da rage tasirin sauyin yanayi .
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana ƙudirinsa na kulla huldar diflomasiyya da gwamnatin Holland a ranar Talata lokacin da ya karbi bakuncin Ms Eva De Wit, babbar jami’an a Ofishin Jakadancin Masarautar Netherland dake Najeriya.
A wata sanarwa da Sanusi Bature Dawakin-Tofa, mai magana da yawun gwamnan ya aikowa kadaura24, ta ce gwamna Yusuf ya jaddada tasirin da masarautar ta samu kan noma da sauyin yanayi a Nahiyar Turai.
Hasashen yanayin da zai kasance yau laraba a birnin Kano da wasu jihohin Nigeria
A cewar sanarwar, Gwamna Yusuf wanda ya nuna sha’awarsa bisa yadda kasar Netherland take gudanar da harkokin noma, ya bayyana aniyar gwamnatinsa na samar da hadin gwiwar don inganta harkokin noma a Kano.
Yusuf ya yi amfani da damar ziyarar ta diflomasiyya wajen bayyana wasu aiyuka da gwamnatinsa ta gudanar bunkasa rayuwar matasa da samar da wadataccen Abinchi a jihar Kano.
Hajjin Bana: Ƙasar Saudiyya Ta Samar Da Wata Lema Ta Musamman Ga Mahajjata
Yayin da yake sanar da tawagar kasar Bakin nasa kokarin da gwamnatin sa ta yi na yakar shan muggan kwayoyi a jihar, Gwamna Yusuf ya ce ya bada umarnin bude cibiyoyin koyar da sana’o’i 24 domin karfafawa matasa gwiwa.
A nata bangaren, Ms De Wit wadda ta samu rakiyar Shugaban Ofishin Jakadancin, Hukumar Kula da Hijira ta Duniya, Mista Laurent De Boeck, ta yi alkawarin hada kai da gwamnatin jihar Kano a fannonin inganta rayuwar matasa, samar da abinci da sauyin yanayi.