Daga Isah Ahmad Getso
Kudurin gyaran dokar masarautun jihar Kano ya samu tsallake karatu na daya a zaman majalisar dokokin jiha a yau Laraba.
Kudurin, ya samu kaiwa wannan mataki ne bayan da Akawun majalisar Alhaji Bashir Idris Diso ya gabatar da karatun Kudurin yayin zaman majalisar.
Hasashen yanayin da zai kasance yau laraba a birnin Kano da wasu jihohin Nigeria
Yanzu dai saura karatu na biyu da na uku, idan kudirin ya tsallake waɗannan matakai to majalisar zata gudanar da gyare-gyare akan dokar, kamar yadda yake a tsarin majalisar.
Yau dai rahotanni sun tabbatar da cewar tun da sanyin safiyar wannan rana ta laraba ne aka jibge tarin jami’an tsaro a harabar majalisar dokokin ta jihar kano domin shirin ko ta kwana.
Hajjin Bana: Ƙasar Saudiyya Ta Samar Da Wata Lema Ta Musamman Ga Mahajjata
Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito a jiya Talata ne dai shugaban masu rinjaye na zauren majalisar ya gabatar da kudurin gaggawa a majalisar domin neman kirawo dokokin masarautun Kano ta shekarar 2019 da kuma ta 2023 domin yi musu gyara.
A Kwanakin baya ne dai kungiyoyi daban-daban suka Rika kira ga majalisar data sake duba Dokar, a gefe guda kuma wasu kungiyoyin na kira ga majalisar da ta yi watsi da bukatar sake duba dokar masarautun ta jihar kano.