Yadda Gwamna Yusuf Ya Siyawa ‘Yan Majalisar Dokokin Kano Motocin alfarma na N2.78bn

Date:

Daga Mubina Mahmoud

 

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sayawa ‘yan majalisar dokokin jihar kimanin su 41 motoci kirar Toyota jeep akan kudi N68m kowannensu.

 

Majiyar kadaura24 ta SolaceBase ta rawaito cewa har yanzu dan kwangilar da aka baiwa siyo motocin bai kai ga kawo rabin Motocin ba.

Motocin da aka kawo an ajiye su a gidajen wasu ‘yan majalisun’’.

Hasashen yanayin da zai kasance yau litinin a birnin Kano da wasu jihohin Nigeria

Kano tana da ‘yan majalisar jiha 40.

Wani fitaccen dan majalisar da ya zanta da SolaceBase bisa sharadin a sakaya sunansa ya bayyana mamakinsa kan yadda wannan jarida ke magana kan lamarin domin abu ne da ba sabo ba gwamnati ta siya wa ‘yan majalisa sabbin motoci.

Me ya sa kuke haka, siyan sabbin motoci sabon abu ne? Gwamnatocin da suka gabata a jihar suma sun yi haka , ”in ji dan majalisar.

Da aka tunatar da shi cewa lamarin ya sha ban-ban da na wancan lokacin duba da kalubalen tattalin arzikin da kasar nan ke fuskanta a halin yanzu, dan majalisar ya mayar da martani inda ya ce kun gane cewa motar za ta saukaka mana wajen gudanar da ayyukan sa ido kuma za a yi amfani da ita wajen gudanar da wasu ayyukan majalisa.

Wata majiya mai tushe ta shaida wa SolaceBase cewa tun da farko Gwamna Abba Kabir Yusuf bai da niyyar siyan motocin ga ‘yan majalisar.

Sai dai kuma da manyan jami’an majalisar suka ziyarci shi anyi zargin cewa sun roki gwamnan ya siya musu ga sabbin motocin n alfarma.

Gwamnan Kano, da sauran gwamnonin arewa maso yamma sun nemi tallafin majalisar dinkin duniya

Da yake zantawa da SolaceBase kan wannan batu , shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin kano, Alhaji Shehu Wada Sagagi ya ce hakkin ‘yan majalisar ne gwamnati ta samar musu da motocin.

“Gwamnan da ya yi la’akari da yanayin tattalin arziki, sai ya fadawa dan kwangilar uma cewa saboda yanayin da ake ciki za’a biya shi kuɗin ne a hankali kuma zai dau tsawon lokaci wanda dan kwangilar ya amince da hakan ,” in ji Sagagi.

Ya kuma jaddada cewa gwamnan ya dauki wannan matakin ne domin mutunta hakkin yan majalisar, kuma haka yake mutunta sauran da hakkokin bangarorin gwamnati.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin gida: Jam’iyyar APC ta Fara Tuhumar Kakakinta na Kano Ahmad S Aruwa

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jam'iyyar APC ta Mazabar Daurawa a...

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...