Daga Abubakar Lawan Bichi
Shugaban riko na karamar hukumar Bichi Alhaji Ahmad Kado Bichi ya ce sun dakatar da dukkanin wani fili da gwamnatin data gabata ta baiwa wasu mutane a karamar hukumar.
Ya ce karamar hukumar ta Bichi bisa umarni gwamnatin jihar Kano ta dakar da dukkan wani filin da aka bayar wanda suka hada Labi inda makiyaya suke Kiwo dabbobi, dajizuka, Makarantu, Asibitoci da dukkan sauran wuraren mallakin gwamnati.
Hasashen yanayin da zai kasance yau Juma’a a birnin Kano da wasu jihohin Nigeria
Alhaji Ahmad Kado yace karamar hukumar ta yi hakanne domin yin adalci ga kowa tare da kira da wanda suke da shaidar mallakar filayen a hannunsu da su gurfana a gaba kwamiti da aka samar kan harkokin kasa domin tantancewa don yin adalci ga kowa.
Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito gwamnatin karamar hukumar ta da gabata ta raba filaye ga wasu mutane a karamar hukumar.