Daga Aliyu Danbala Gwarzo
Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta sanar da samun afkuwar gobara 222 a sassan jihar tsakanin watan Janairu zuwa Maris.
Jami’in hulda da jama’a na hukumar kashe gobara ta jihar, Saminu Abdullahi, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) a Kano, cewa lamarin ya shafi gidajen zama, shaguna da gidajen mai.
Abdullahi ya ce mutane 16 ne suka rasa rayukansu a lokacin da lamarin ya faru yayin da jami’an hukumar suka ceto wasu mutane 43.
Hasashen yanayin da zai kasance yau talata a birnin Kano da wasu jihohin Nigeria
“Mutane 16 ne suka rasa rayukansu, yayin da gobara ta salwantar da dukiya ta akalla Naira miliyan 176,” inji shi.
Jami’in ya ce an kuma ajiye kadarorin da ya kai Naira miliyan 332 a lokacin da ake tantancewa.
A cewar sa, ma’aikatar ta amsa kiraye-kirayen gaggawa na Iftila’i guda 43 da kuma wayar karya guda 32 daga mazauna jihar.
Gwamnatin Kano Zata Fara Karrama Malaman Makaranta Masu Kwazo
Abdullahi ya kara da cewa galibin tashin gobarar na faruwa ne sakamakon rashin amfani da na’urorin lantarki yadda ya dace.
Ya shawarci mazauna jihar Kano da su rika kashe iskar gas da silinda a duk lokacin da ba a amfani da su, domin gujewa barkewar gobara a gidaje.