Hasashen masana yanayi ya nuna cewa yau talata 14-05-2024 dai-dai da 6 ga watan Dhul-Qada 1445 A.H , idan Allah ya so za’a sami zafin Rana a jihar Kano wanda zai kai 40 bisa ma’aunin zafi.
A jihar Kano dai babu yiwuwar samun ruwan Sama .
Kadaura24 ta rawaito yanayi ranar zai kasance mai zafi sosai, Inda ranar zata fara zafi sosai daga misalin karfe 12 na rana har zuwa karfe 6 na yamma Sannan yanayin ya Sauya.
Yan sanda a Kano na bincike kan mutuwar jami’in kwastam da ake zargin ya kashe kansa
Hasashen dai ya nuna cewa ranar zata fara zafi ne daga lokaci da zafin ranar ya kai 39 inda zai sauya zuwa 40 bisa ma’aunin zafi.
Jihar Kano dai na fuskantar tsananin zafi a yan Kwanakin nan, Wanda hakan yasa masana suke baiwa al’umma mazauna jihar shawarar yadda zasu kare kan su daga illar da zafin ranar ka iya yi musu.
Shawarwarin da likitoci suke bayarwa sun hadar da takaita shiga Rana, yawaita shan ruwa, sanya kaya masara nauyi da dai sauransu.
Mai magana da yawun gwamnan Kano Sanusi Bature ya tallafawa mata 100
Kaduna hasashen ya nuna a jihar Kaduna zafin rana zai kai 35 bisa ma’aunin zafi.
Abuja Kuna hasashen ya nuna zafin ranar zai kai 34 bisa ma’aunin zafi
Jihar Yobe kuma hasashen ya nuna cewa zafin rana zai kai 42 bisa ma’aunin zafi.
Jihar Kebbi ita kuwa zafin ranar zai kai 41 bisa ma’aunin zafi .
Birnin maiduguri na jihar Borno zafin ranar zai kai 41 bisa ma’aunin zafi.
Ku biyo mu gobe don kawo muku yadda hasashen zai kasance