Wani Yaron Ya Sayar Da Ƙodarsa Ya Sayi Wayar Hannu

Date:

Daya daga cikin yaran da aka cirewa ƙoda a wani asibiti a Abuja ya je sayen wayar salula ta kimanin naira 290,000 kwanaki bayan sayar da ƙodarsa.

Wani mai sayar da waya a kasuwar Mararraba da ke Jihar Nasarawa, Abdullahi Mohammed ne ya shaida wa Babbar Kotun Abuja yayin da ya bayyana a matsayin daya daga cikin shaidun da aka gabatar mata a ci gaba da shari’ar takaddamar cin kasuwar ƙoda a babban birnin Nigeria.

Abdullahi Mohammed ya shaida wa kotun cewa, Oluwatobi Salmon Adedoyin ya zo shagonsa ne a ranar 20 ga Fabrairu, 2023 don siyan wayar har ta kusan Naira 290,000.

Hasashen yanayin da zai kasance yau Asabar a birnin Kano da wasu jihohin Nigeria

Da yake gabatar da shaidar a ranar Alhamis, lauyan masu ƙara, Hassan Tahir Esq ya ce Abdullahi Mohammed wanda aka je sayen wayar salular a shagonsa ya bai wa yaron bayanan asusun ajiyarsa na banki inda aka tura masa kuɗi Naira 500,000.

“Na tambaye shi dalilin da ya sa ya biya ni fiye da kima, sai ya ba ni asusun ajiyarsa na bankin Opay don in mayar da kuɗin da ya kai Naira 210,000 ya tafi abinsa,” in ji Abdullahi.

Dalilan da suka sa aka rufe makarantar Legal ta kano

Tun da farko, lauyan mai ƙara, Tahir ya sanar da kotun cewa ba zai iya kammala gabatar da hujjojinsa ba saboda rashin halartar jami’in da ke bincike a kan lamarin.

Hakazalika, lauyan wanda ake ƙara, Afam Osigwe (SAN) ya buƙaci kotun da ta sauya ranar ci gaba da sauraron ƙarar zuwa lokaci na gaba domin samun damar tattaro hujjojinsa.

Dangane da wannan bukatar ce mai shari’a Kezziah Ogbonnaya ya ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 21 da 22 ga watan Mayu.

Ana iya tuna cewa, Hukumar Hana Fataucin Mutane Ta Ƙasa (NAPTIP) ce ta gurfanar da wasu ma’aikata huɗu na asibitin Alliance and Service Ltd a gaban ƙuliya, ciki har da Dakta Christopher Otabor da Emmanuel Muyiwa Olorunlaye da Chikaodili Ugochukwu da kuma Dakta Aremu Abayomi a kan tuhume-tuhume 11 da ke da alaƙa da safarar sassan jiki ba bisa ƙa’ida ba.

Wannan na zuwa ne dai bayan wani rahoton fallasa da Jaridar Daily Trust ta wallafa bayan ta bankado yadda ake cinikin sassan jikin mutum a Abuja da Jihar Nasarawa bayan bincike da tattaunawa da waɗanda abin ya shafa.

 

Daily Trust

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...

Bai dace ɗalibai su rika murnar kammala karatu ta hanyoyin da ba su dace ba – Mal Ibrahim Khalil

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa ‎ ‎ ‎Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano...

Budaddiyar Wasika ga Gwamnan Kano kan wanda zai maye gurbin Muhuyi Magaji R/gado daga Kungiyar Lauyoyi yan Kano

Zuwa ga Mai Girma Alhaji Abba Kabir Yusuf Gwamnan Jihar Kano Gidan...