Daga Rahama Umar Kwaru
Rundunar ‘yan sandan jihar Kano tana sanar da daukacin al’umma cewa jami’an rundunar ‘yan sanda mai lamba 52 (PMF) Squadron dake Challawa Kano za su gudanar da atasayen harbi na kwanaki biyu a Hawan Kalibawa dake karamar hukumar Dawakin Tofa a jihar Kano. daga karfe 6 safe zuwa 6 na yamma kullum a Asabar, 11th da Lahadi 12th ga watan Mayu 2024.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda jama’a na rundunar SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya sanyawa hannu kuma aka rabawa manema labarai.
Iftila’i: Jarumar Fim din Labarina ta yi hatsari tare da mijinta
Sanarwar ta shawarci jama’a musamman mazauna kauyukan Dambazau, Gangaren Dutse, Tumfafi, Kakurum da Dandalama a kananan hukumomin Dawakin Tofa da Ungogo da kewaye da su nisanta daga wajen, kuma kada su firgita da karar harbe-harben atasayen da zasu gudanar.
Kwamishinan ‘yan sanda CP Mohammed Usaini Gumel, FIPMA, psc, ya yabawa al’ummar jihar Kano bisa fahimtar juna, addu’o’i, goyon baya da hadin kai da suke baiwa rundunar a koda yaushe.