Daga Nasiru Ahmad Sadiq Wanda kuma Malami ne a makarantar ta College of Islamic And Legal Studies.
Mun yi mamaki matuƙa bayan fitowar wani rahoto da Freedom Radio ta fitar game da dambarwar da ta taso a Legal. Rahoton wanda aka saka irinsa a shafin Mai Girma Kwamishinan Ma’aikatar iIimi Mai Zurfi ta Jihar Kano ya bayyana cewa ‘wai’ wasu mutane ne suke ƙoƙarin ganin an cire kalmar ‘Islamic’ daga sunan kwalejin, yayin da ita kuma gwamnati ta doge akan ba za a cire ba.
2. Wato a gaskiyar zance babu wani abu mai kama da wannan lamari a Legal. Kuma ba wannan ne ƙudurin ma’aikatan wannan kwaleji ba. Bamu san da wannan magana ba domin ba ita ake yi ba.
3. Ƙudurinmu shi ne a ɗaga likkafar wannan kwaleji zuwa cikakkiyar kwalejin ilimi da shari’a wato College of Education and Legal Studies kamar yadda aka yiwa sauran takwarorinta na Ringim, Misau, Nguru da Daura.
Dalilan da suka sa aka rufe makarantar Legal ta kano
4. Abu kamar raha ace a ƙarni na 21 a ji wani yana iƙirarin wai za a cire kalmar Islamic daga sunan wata makaranta don wata manufa ta rashin addini. Kuma wai a garin Kano, a makarantar da saboda da jinginuwa da addini ake ce mata makarantar Islamiyya. Haba don Allah. A ƙaddara ma akwai waɗanda suke yunƙurin hakan, ta ina cire kalmar Islamic ɗin zai bayu izuwa ga sauya manufar da ake kai ta ganin bunƙasar makarantar? Shin ba a yin kwasa-kwasan da suka shafi addini a Bayero da ABU da wasu jami’o’in ƙasar nan alhali babu kalmar Islamic a jikin sunayensu?
Muhimmiyar Sanarwa Daga Rundunar Yan Sandan Jihar Kano
5. Jami’ar Ummul Qura dake Makka na da tarihi iri ɗaya da Legal. Lokacin da aka kafa ta a shekarar 1949, an kafa ta ne a matsayin kwalejin koyar da darussa na Shari’a Musulunci da kuma darussan Larabci. A yau, bunƙasarta ya kai ta zama jami’a wacce ake koyar da darussa masu yawa waɗanda ba don su aka kafata ba asali. Kuma har yau tana daga cikin jami’o’i a duniya da ake alfahari dasu wajen koyar da darussan Musulunci. Duk da haka a sunan jami’ar babu kalmar ‘Islamic’.
6. Zan so sanin shin kalmar Education ana jinginata ga ilimin da ya shafi boko ne kaɗai ko kuwa ilimin komai ma zai iya shiga har da na addini? Baki ɗayanmu mun san amsar nan. Yau idan aka mayar da Legal ta zama College of Education shin Islamic Studies da ake yi a cikinta ba za a iya kiransa Islamic Education ba?
7. Magana ta gaskiya ita ce, babu wanda yake hanƙoron ganin an cire kalmar Islamic daga sunan Legal. Idan kuma har akwai a Legal to ya kamata Mai Girma Kwamishina ya bayyanawa mutane su waye? Mu dai bamu san ko su waye ba. Kuma wannan gwagwarmaya da muke yi gaɓa ɗaya muke yinta daga daga malaman addinin cikinmu har malaman bokon.
8. Amfani da kafafen yaɗa labarai wajen faɗawa jama’a cewa wai wasu daga cikin malaman Legal na ƙoƙarin ganin an cire Islamic daga sunan Legal farfaganda ce kawai da kokarin haɗa malaman Legal da al’ummar Jihar kano. Jama’a su sani dukkan Malaman Legal Musulmai ne masu kishin addini kuma masu ilimi da tarbiyya. Kuma burinmu ganin ci gaban Legal da ɗalibanta.
9. Daga cikin abinda ya karfafa mana gwiwa muke ƙoƙarin ganin mun samu ɗagawar likkafa shi ne yadda dole muke amfani da kuɗaɗenmu wajen halartar conferences da seminars da kuma publication a journals. Da waɗannan ake yi mana promotion. Idan bamu samu kuɗi mun yi ba, ba za ai mana ba. Don haka muka ga ya kamata kamar kowace kwaleji muma mu samu agaji daga TETFUND. TETFUND kuma babu mai cin moriyarta sai wanda ke ƙarƙashin wasu hukumomi wacce NCCE tana ciki. To burin Legal ta kasance ƙarƙashin kulawar NCCE ɗin. Ita kuma sai makaranta ta kasance College of Education tukunna zata karɓeta. To meye laifin hakan? Makantar nan kowa ya san marainiya ce. Ta dogara kacokan da abinda gwamnati take bata. Idan Mai Girma Kwamishina bai tallafa mata ta bunƙasa ba waye zai tallafa mata?
10. Na san jama’a da yawa basu sani ba amma bari na ƙara muku sani game da wani abu akan Legal. A rubutuna na baya na bayyana cewa muna da masu PhD sama da 80, muna da masu digiri na biyu sama da 200. Shin kun san cewa waɗannan mutanen kaso 95 na cikinsu da kuɗaɗen aljihunsu suka yi waɗannan digirori? Ma’ana babu wani intervention daga gwamnati ta hanyar TETFUND. Da yawa daga cikinsu sun siyar da kadarorinsu ne, wasu sun ci bashi don yin karatu a gida da wajen Najeriya.
11. Haka zalika mu ‘yan Kwankwasiyya ne. Kuma masu tsananin kishinta. Kuma mun san kyakkyawar manufar tsarin Kwankwasiyya akan ci gaban ilimi. Don sanin hakan ne ma yasa muka zaɓi gwamnatin Kwankwasiyya kuma muka sanya jama’armu suka zaɓe ta. Mun tabbatar gwamnatin Mai Girma Gwamna Engr. Abba Kabir Yusuf ba zata taɓa sauka daga gwadaben da Jagora Dr. Rabiu Musa Kwankwaso ya ɗora mu akai ba.
12. Muna ƙara jaddada ƙudurinmu cewa idan muka rasa samun mafita daga wannan al’amari da ya hana mu bacci ya hana mu walwala, zamu kai kokenmu kai tsaye zuwa ga Mai Girma Gwamna Engr. Abba Kabir Yusuf da kuma Ubanmu, Jagoranmu Engr. Dr. Rabiu Musa Kwankwaso. Mun tabbatar su zasu share mana hawayenmu.
12. Muna ƙara kira ga Mai Girma Kwamishina, a tsaya a duba wannan lamari da kyau. Kar ya yarda tarihi ya tuna da shi a matsayin wanda Legal ta rasa wani alheri a lokacinsa. Kuma muna ƙara tuna masa cewa da mu da shi uwarmu ɗaya ubanmu ɗaya. Ƙauna ce tasa muke tuna masa amfanin wannan lamari. Kuma sai yafi kowa alfahari ace a lokacin da yake Kwamishina aka ɗaga likkafar Legal.
Ina masa fatan alkhairi.
Alaramma Mamman Naso