Zargin batanci: Sheikh Abduljabbar ya Nemi Gwamnatin Kano ta biya shi Naira miliyan 20

Date:

Daga Halima Musa Sabaru

 

Kotun daukaka kara dake zaman ta a sakatariyar Audu Bako a Kano, ta dage ci gaba da sauraren shari’ar da Abduljabbar Nasir Kabara, ya daukaka kan hukuncin kisa ta hanyar rataya, da babbar kotun shari’ar addinin musulinci dake zaman ta a Kofar Kudu, ta yanke masa bisa samun da laifin yin batanci ga fiyayyen halitta Annabi Muhammed Sallallahu Alaihi Wassalam.

Kotun daukaka karar karkashin jagorancin, justice Nasiru Yusuf da kuma A’isha Mahmud , sun saurari karar a Ranar Litinin nan.

Lauyan Abduljabbar Nasiru Kabar, Barista Yusuf Sadik, ya shaida wa kotun cewar a shirye suke don ci gaba da sauraren shari’ar.

Abubuwan da ya kamata yan Arewa su yi don amfana da mulkin Tinubu – Kwankwaso

Sai dai lauyan gwamnatin Kano Barista Bashir Saleh, ya roki kotun da ta kara mu su lokaci kafin a ci gaba da sauraren shari’ar.

Lauyan Abduljabbar Nasiru Kabara, ya nuna rashin jin dadinsa , sakamakon yace tun tuni ya sada lauyan gwamnatin da takaddun martaninsu tun a watan Fabarairun 2024, inda ya nemi gwamnatin Kano ta biyashi naira miliyan 20 , sakamakon bata masa lokaci da aka yi.

Iftila’i: Gobara ta Tashi a Gidan Tsohon Gwamnan Jihar Kano

Alkalan kotun, Justice Nasiru Saminu da Justice A’isha Mahmud, sun bincika takaddun da lauyan Abduljabbar Nasiru Kabara, ya yi ikirarin ya sadar da lauyan gwamnatin Kano, inda aka gano cewar a watan Maris ya ba wa lauyan gwamnatin takaddun martanin .

Daga bisani lauyan Abduljabbar Nasiru Kabara, ya janye bukatar Neman Gwamnatin ta biya shi naira miliyan 20.

Alkalan kotun daukaka karar sun dage ci gaba da sauraren shari’ar, zuwa Ranar 9 ga watan Mayun 2024, don ci gaba da sauraren shari’ar.

Idon Gari

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin gida: Jam’iyyar APC ta Fara Tuhumar Kakakinta na Kano Ahmad S Aruwa

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jam'iyyar APC ta Mazabar Daurawa a...

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...