Gwamnatin Kano ta Magantu Kan Harbin Da Aka Yiwa Wani Dan Jarida a Gidan Gwamnatin jihar

Date:

Daga Mubina Mahmoud

 

Gwamnatin jihar Kano ta musanta labarin dan jaridar gidan talabijin na ARTV da harsashi ya same shi a gidan gwamnati a daren Juma’a.

Kadaura24 ta ruwaito cewa, wani dan jarida dake wakiltar gidan talabijin na Abubakar Rimi, a gidan gwamnatin Naziru Idris Ya’u, ya sami rauni sakamakon harbin bindiga a yammacin ranar Juma’a, a gidan gwamnati.

Ba a San dai ta inda akai harbin ba, Amma tuni aka garzaya da dan jaridar da ya jikkata zuwa asibitin gidan gwamnati.

Harbin Bindiga: Wani Dan Jarida ya Tsallake Rijiya da Baya a Gidan Gwamnatin Kano

Sai dai a cikin wata sanarwa da Sanusi Bature Dawakin Tofa, Mai Magana da yawun gwamnan jihar , ya fitar a ranar Asabar, ya musanta faruwar lamarin inda ya bayyana shi a matsayin labari mara tushe.

Sanarwar ta kara da cewa, “An jawo hankalin gwamnatin jihar Kano kan wani rahoton daya fito daga kafafen yada labaran yanar gizo da ke nuna cewa wani harsashi ya sani wani dan jarida dake wakiltar gidan talabijin din ARTV a gidan gwamnatin jihar.

Hasashen yanayin da za’a tashi da shi a gobe Asabar a Birnin Kano da wasu jihohin Nigeria

Labari ya Sanya fargaba da kuma cece-kuce game da lafiyar ‘yan jarida da ke wakiltar ARTV a gidan gwamnati.

‘’magana ta gaskiya, Naziru Yau, wakilin gidan talabijin na jiha, babu wani harsashi da ya same shi”.

‘’Maimakon haka, ya samu raunuka daga tarkacen karfunan da ake fito da su daga wani gini da ake gyara a gidan gwamnatin jihar Kano.

Sai dai binciken da Majiyar KADAURA24 ta SolaceBase ta gudanar ya nuna cewa lamarin ya afku ne a masallacin da ke kusa da kofar shiga gidan gwamnati a daidai Inda aka kebe domin yin alwala, kamar yadda wanda abin ya shafa ya tabbatar.

Magana ta gaskiya, babu wani gini da ake yi a kusa da wajen sai dai aikin da ake yi a can bayan ofishin gwamna da ke kusa da African House a gidan gwamnati.

An sanar da SolaceBase tabbatacce cewa an kuma kai wakilin asibiti a safiyar yau don ci gaba da kula da shi.

Sai dai ana ci gaba da bincike kan dalilin yin harbin da kuma daga Ina aka harbo harsashin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin gida: Jam’iyyar APC ta Fara Tuhumar Kakakinta na Kano Ahmad S Aruwa

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jam'iyyar APC ta Mazabar Daurawa a...

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...