Daga Aminu Yahaya Tudun wada
Dillalan filaye a Hotoro da ke birnin Kano sun danganta tashin farashin fili a yankin da samuwar Jami’ar Maryam Abacha da ke Kwanar Maggi a yanki.
Daya daga cikin dillalan filayen, Muhammad Najume ne ya bayyana hakan a yayin wata ganawa da yayi da Kadaura24. Inda ya ce tashin farashin ya fara ne bayan da jami’ar ta fara aiki .
Malam Muhammad ya bayyana cewa filin da ake sayar da shi kan Naira miliyan 20 a shekarar 2023 a yanzu ana sayar da shi a kan Naira miliyan 150 ko sama da haka.
Wannan za a iya danganta shi da yanayin tattalin arziki da kuma samuwar jami’ar a yankin.
Da dumi-dumi: NNPC ya sanar da ranar da Zai kawo karshen ƙarancin man fetur a Nigeria
Jami’ar Maryam Abacha Ta Kawo Cigaba Mai Dorewa a Unguwar Hotoro, Kawo Da Dukkanin Jihar Kano Baki Daya
Cikin Wani Bincike da Aka Gudanar Ya Nuna Yadda Gidaje da Filaye Sukayi Daraja Tare da Samun Arziki Mai Dorewa a unguwar Hotoro da Kawo a Cewar Wani Dillalin Gidaje da Filaye Mallam Muhammadu.
Yace Ansamu Darajar Kashi 40 cikin 100 Na Gidaje da Filaye Sanadiyar Zuwan Jami’ar Maryam Abacha.
Mallam Muhammad Ya Bayyana Yadda Kasa ta kara Darajar Kashi 30 cikin 100.
A nasu bangaran suma mazauna yankin sun ce tabbas sun samu cigaba, sannan ya’yansu sun samun aiki tare da samun Ingantaccen tsaro titina da hanya tare da Samun wutar lantarki da Ruwan Famfo Sanadiyar Jami’ar Maryam Abacha.
Sojoji sun tarwatsa maɓoyar ƴanbindiga, sun kuɓutar da mutane a Taraba
Ta fuskantar kasuwanci wani Malam Usman Yahaya yace sun sami cigaba sakamakon yadda daliban jami’ar suke sayan kayansu.
Sai kuma Wata yar kasuwa mai suna Angelina nai sayar da masara ta yi bayanin cewa tana samun ciniki sosai ba kamar baya ba
Alh Ibrahim Kalamuwahid Ya Bayyana Cewa Kasuwancinsu ya karu da Kashi 50 cikin Dari.
Suma dalibai sun bayyana farin cikin su da samun gurbin karatu a Jami’ar Maryam Abacha da kuma yadda al’umma Mazauna Yankin ke Musu faran-faran cikin girmamawa.