Sojoji sun tarwatsa maɓoyar ƴanbindiga, sun kuɓutar da mutane a Taraba

Date:

 

Dakarun Najeriya da ke aiki ƙarƙashin rundunar murƙushe ayyukan ƴanbindiga a jihar Taraba ta Whirl Stroke sun tarwatsa wani sansanin ƴanbindiga inda suka kuɓutar da mutanen da aka yi garkuwa da su tare da gano tarin makamai da alburusai.

Rundunar sojin Najeriyar ce ta wallafa hakan cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X.

A cewar sanarwar, dakarun da aka girke a Fikyu, a ranar 29 ga watan Afrilu sun kai ɗauki kan wasu rahotanni da suka samu cewa wasu da ake zargi ƴanbindiga ne sun buɗe wuta a yankin Pukun da ke Fikyu a ƙaramar hukumar Ussa. Sojojin sun yi musayar wuta da su har suka samu galaba a kansu.

Da dumi-dumi: NNPC ya sanar da ranar da Zai kawo karshen ƙarancin man fetur a Nigeria

Ƙarin binciken a yankin ya sa sojoji sun gano bindiga ƙirar AK47 da ƙunshin alburusai.

Kazalika, sojojin da aka tura Kufai Amadu da Kasuwan Haske tare da haɗin gwiwar sojoji daga runduna ta ɗaya sun ɗauki mataki kan wani bayanin sirri da suka samu game da maɓoyar ƴanbindiga a ƙauyen Vingir da ke ƙaramar hukumar Katsina Ala a jihar Benue. A nan ma sojojin sun yi arangama da ɓatagarin inda suka murƙushe su.

Sojoji sun kama wani da ake zargi mai garkuwa da mutane ne da aka same shi da wayoyin hannu biyu ƙirar Techno da kuɗi naira dubu 40.

An yi bincike a sansaninsu inda kuma aka gano bindiga ƙirar AK47 sannan aka samu kuɓutar da Dakta James Raphael da ɗansa a Gbeji a ƙaramar hukumar Ukum da ke jihar Benue.

Gwamnatin Tarayya ta bayyana nasarori data samu sakamakon cire tallafin man fetur a Nigeria

Sanarwar ta kuma ce sojojin da ke aiki a bataliya ta 20 sun kama wani mutum a ƙaramar hukumar Bali da ke jihar Taraba tare da buhu huɗu na wani abu da ake tunanin tabar wiwi ce.

Rundunar ta ce mutumin ya daɗe ana neman shi ruwa a jallo saboda yadda yake ta’amali da miyagun ƙwayoyi da kuma samar wa ƴan bindiga da sauran masu laifi miyagun ƙwayoyi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yanzu-yanzu: Dangote ya rage farashin man fetur a Nigeria

Matatar mai ta dangote ta rage farashin man fetur...

Muna bukatar kayan aiki domin magance matsalar tsaro a karamar hukumar Nasarawa – Muhd Haruna Black

Kwamandan Jami'an sintiri na karamar hukumar Nasarawa a jihar...

Da dumi-dumi: An Sanya dokar Hana fita a Kaduna

Gwamnatin Kaduna ta sanya dokar taƙaita zirga-zirga ta tsawon...

Yanzu-Yanzu: An ɗage jana’izar Aminu Ɗantata saboda wasu dalilai

Gwamnatin Najeriya ta sanar da ɗage jana'izar fitaccen ɗankasuwar...