Zargin Almundahana: Gwamnatin Kano Ta Fara Bincikar Shugaban Gidan Talabijin Na ARTV

Date:

Daga Mubina Mahmoud

 

Hukumar Karɓar Ƙorafe-Ƙorafe da Yaƙi da Rashawa ta Jihar Kano, PCACC, ta ƙaddamar da bincike dangane da zargin almundahana kan Shugaban Gidan Talabijin na jihar (ARTV), Alhaji Mustapha Adamu Indabawa.

Binciken na zuwa bayan ƙorafin da Ƙungiyar ’Yan Jarida (NUJ) da Ƙungiyar Ma’aikatan Gidajen Rediyo da Talabijin (RATTAWU) suka gabatar wa Gwamna Abba Kabir Yusuf.

Ƙungiyoyin na zargin Alhaji Indabawa da almundahanar kuɗin da suka kai Naira miliyan ɗari da kuma saɓa ka’idar aiki.

Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito  Indabawa na ɗaya daga cikin shugabannin hukumomi da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya naɗa a watannin baya bayan nan.

Kungiyoyin Yan Jaridu na ARTV sun koka da barazanar da MD ke yi musu da zargin sayar da gidajen ma’aikata

Bayanai sun ce masu binciken sun titsiye Alhaji Indabawa a ranar Juma’ar da ta gabata kan zargin sama da-faɗin fiye da Naira miliyan 60 da kuma zargin satar tsabar kuɗi har Naira miliyan uku na Asusun Tallafa wa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNICEF) da ya yi ikirarin an sace a cikin motarsa.

Duk laifukan da ake zargin Alhaji Indabawa sun ci karo da sashe na 26 na Kundin Dokokin hukumar PCACC kuma mafi ƙanƙantar hukuncin shi ne cin sarƙa ta shekara uku.

A yayin da Aminiya ta tuntubi Alhaji Indabawa dangane da taƙaddamar, ya ce ba shi da ta cewa tunda har lamarin yana gaban hukuma.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

An Dauke Shaikh Abduljabbar Daga Gidan Yari na Kurmawa Zuwa Wani Wuri – Yan uwansaba

Wani labari da ke yawo a kafafen sada zumunta...

Majalisu na neman sauya lokacin zabuka a Nigeria

Majalisar Dokoki Ta Ƙasa Ta Gabatar Da Kudirin Sauya...

Kungiyar Lauyoyi yan asalin jihar Kano sun mika korafi ga kasashen Amuruka Ingila da UN kan zargin kisan a Tudun Wada

Kungiyar Lauyoyin Yan Asalin Jihar Kano (National Forum of...

Da dumi-dumi: ASUU ta sanar da ranar da zata fara yajin aiki

Shugabancin Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya (ASUU) ta umurci...