Daga Sani Danbala Gwarzo
Jam’iyyar NNPP tace ta ga dacewar dole ta yi magana kan munanan kalaman Cif Boniface Aniebonam, tsohon dan jam’iyyar da aka kora.
“Yana da kyau a bayyana cewa korar tasa tare da wasu daga cikin ’yan uwansa, ta kasance ne sakamakon abubuwan da suka yi wadanda suka wuce gona da iri, da kuma dakile ci gaban jam’iyyar gaba daya, kuma sai da aka bi doka Sannan aka koresu daga jam’iyyar*.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Sakataren yada labaran jam’iyyar NNPP na kasa Ladipo Johnson ya sanyawa hannu kuma aka aikowa kadaura24.
Yadda akai Rarara ya yi min waƙa – Fatima Mai Zogale
Sanarwar ta ce tun a wancan lokaci Aniebonam da sauran su sun shigar da karrarkin a gaban kotuna domin kalubalantar hukuncin da jam’iyyar ta yanke musamman kan korar su. Sun kuma bukaci kotun da ta tilasta wa INEC ta amince da su a matsayin Sahihancin yan jam’iyyar ta NNPP.
“To sai dai kuma, ya zuwa yanzu, duk irin wannan mataki na shari’a da suka rika dauka ya ci tura, kuma kotuna daban-daban sun yanke shawarar amincewa da jam’iyyar NNPP a matsayin jam’iyyar siyasa, karkashin ingantacciyar jagorancin Dakta Ahmed Aduji”.
Sanarwar ta kara da cewa matakin da ya dace ga Aniebonam da abokan tafiyarsa shi ne su daukaka kara game da hukuncin da kotu ta yanke musu amma sai suka koma yin kalaman batanci, yaudara da kuma karyata ga jagoran jam’iyyar na kasa da kuma Shugabancin jam’iyyar.
Hukumar NEMA ta Bayyana Adadin Wadanda Suka Rasu a Hatsarin Ginin da Afkawa wasu a Kano
Yanzu, Aniebonam na ikirarin mallakar jam’iyyar ne kawai amma wannan ba gaskiya ba ne , kuma hakan ya sabawa dokar. Kundin tsarin mulkin Tarayyar Najeriya ya fito karara yayi bayani a kan mallakar jam’iyya da zama yan jam’iyyar, mutum daya ba zai iya mallakar jam’iyyar bajam’iyya ba, sai dai gamayyar mutane.
NNPP na son sanar da jama’a cewa ta bi dukkanin matakai na Shari’a kafin ta kori Boniface daga jam’iyyar ta NNPP.