Hukumar NEMA ta Bayyana Adadin Wadanda Suka Rasu a Hatsarin Ginin da Afkawa wasu a Kano

Date:

Daga Halima Musa Sabaru

 

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa NEMA ta tabbatar da mutuwar mutane uku tare da jikkata wasu biyu a wani gini mai hawa uku da ya rufta a unguwar Kuntau da ke karamar hukumar Gwale a Kano.

Dokta Nuradeen Abdullahi, kodinetan hukumar NEMA na Kano, ya tabbatar da faruwar lamarin da kuma adadin wadanda suka mutu a ranar Juma’a a Kano.

“Mun sami kiran waya mai cike da damuwa yau da misalin karfe 9:20 na safe daga wani mutum cewa wani gini mai hawa uku da ake ginawa ya ruguje a unguwar Kuntau”.

Iftila’i: Wani Gini ya Fado Kan Magina 12 a Kano

“Ya zuwa yanzu, an ceto mutane biyar, kuma an kai su Asibitin kwararru na Murtala Muhammad, inda aka tabbatar da mutuwar uku daga cikinsu, yayin da wasu biyu suka jikkata suka samu raunuka, kuma suke samun kulawa.” Inji Abdullahi.

Ya kara da cewa har yanzu ana ci gaba da aikin ceto wadanda suka makale a cikin buraguzan ginin.

“Tawagar NEMA da hukumar kashe gobara ta jihar Kano da ‘yan sanda da Red Cross da NSCDC da SEMA da dai sauran su na nan a wurin da lamarin ya faru domin tabbatar da fito da sauran mutanen da suka makale,” in ji Abdullahi

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yadda kamfanin ganyen shayi na Z&Y ke fuskantar matsin lamba daga TOP TEAA

Wani matashin ɗan kasuwa daga jihar Kano, mai suna...

Gwamnatin Kano ta bayyana sunayen unguwannin da aka sami gurbatacciyar Iska

    Wani rahoto na mako-mako kan yanayin lafiyar iska da...

Sallah: Gwamnatin Kano za ta hukunta gidan wasan da ya bar masu shigar banza da shaye-shaye

Daga Rahama Umar Kwaru   A kokarin ta na yaki da...

Sallah: Hussari ya sauke kabakin arziki ga yan jam’iyyar APC na karamar hukumar Gwale

Daga Ibrahim Abubakar Diso   Tsohon Dan Majalisar wakilai da ya...