Hukumomi a jihar Kano sun fitar da wasu jerin shawarwari ga al’umma mazauna jihar kan yadda za su kare kansu daga yanayin da ake ciki na tsanani zafi.
Wannan na zuwa ne bayan an samu rahoton ƙaruwar zazzaɓi mai zafi da hukumomin lafiya a jihar suka danganta da ƙaruwar yanayin da kaɗawar busasshiyar iska.
Bayanai na cewa irin wannan yanayi da aka shiga ya haifar da mutuwar mutum fiye da 40 a jihar, sannan da dama suna cikin mawuyacin hali.
Da yake zantawa da BBC Hausa, Kwamishinan Lafiya na jihar kano Dr Abubakar Labaran Yusuf ya ce jami’an da suka tura don gudanar da bincike sun gano cewa tsananin zafin da ake fama da shi ne ya haddasa zazzaɓi mai zafi ga wasu daga cikin al’ummar jihar.
A cewarsa, babu mamaki zazzaɓin ne ya jawo mace-macen da aka gani a wasu garuruwa kamar Gundutse a ƙaramar hukumar Kura a makon jiya.
Dr Labaran ya ce rahotannin da suka samu sun nuna cewa an fara ganin ƙaruwar zazzabin mai zafi da kuma mace-mace ne tun fa arkon watan jiya.
Shawarwarin su ne kamar haka:
1. Mutane su guji shiga cincirindon jama’a
2. Mutane su guji kwana a dakin da yake da mutane da yawa
3. Mutane su guji shiga cikin rana musamman lokacin da ranar ta take.
4. Yana da Kyau mutane su rika yawaita shan ruwa domin yawan gumin da suke yana kone ruwan jikinsu.
5.yana da kyau wadanda shiga ranar ya zaman musu dole su rika amfani da malafa.