Kamfanonin Sadarwa na neman izinin kara kuɗin kiran waya a Nigeria

Date:

Daga Ibrahim Husaini Dorayi

 

Kamfanonin sadarwar da ke aiki a Najeriya musamman Glo, MTN, Airtel da 9Mobile suna rokon gwamnatin tarayya da ta sahalle musu su kara kuɗin kiran waya domin bunkasa aiyukan su.

A cewar kamfanonin farashin da ake amfani da shi a yanzu bai dace da yanayin tattalin arziki da ake ciki, don haka suke neman izinin gwamnati don kara kuɗin kiran wayar.

Kamfanonin sadarwa guda hudu sun ce su kadai ne ba su kara kudi akan al’amuran su ba wanda hakan ke barazana ga dorewar masana’antar da kuma yiyuwar sanyaya gwiwar masu zuba jari.

Sanarwa ta Musamman Daga Hukumar Samar da Ruwan sha ta Jihar Kano

Sun bayyana hakan ne a cikin wata sanarwar hadin gwiwa da kungiyar masu lasisin sadarwa ta Najeriya (ALTON) da kungiyar kamfanonin sadarwa ta Najeriya (ATCON) suka fitar ranar Alhamis.

Tsakananin zafi: Hukumomi a Kano sun ba da shawarwarin kare kai ga al’umma

A cewar sanarwar mai dauke da sa hannun shugaban ALTON, Mista Gbenga Adebayo, da shugaban ATCON, Mista Tony Emokpere, ba a yi wani kari kan farashin kiran waya na bai daya ba a cikin shekaru 11 da suka gabata.

Sun danganta rashin kara kuɗin kiran ga ka’idojin da aka gindaya musu duk da mummunar matsalar tattalin arziki da ake fuskanta a ƙasar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

An Dauke Shaikh Abduljabbar Daga Gidan Yari na Kurmawa Zuwa Wani Wuri – Yan uwansaba

Wani labari da ke yawo a kafafen sada zumunta...

Majalisu na neman sauya lokacin zabuka a Nigeria

Majalisar Dokoki Ta Ƙasa Ta Gabatar Da Kudirin Sauya...

Kungiyar Lauyoyi yan asalin jihar Kano sun mika korafi ga kasashen Amuruka Ingila da UN kan zargin kisan a Tudun Wada

Kungiyar Lauyoyin Yan Asalin Jihar Kano (National Forum of...

Da dumi-dumi: ASUU ta sanar da ranar da zata fara yajin aiki

Shugabancin Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya (ASUU) ta umurci...