Iftila’i: Gobara ta tashi a filin jirgin saman Legas

Date:

Hukumar kula da filayen tashi da saukar jiragen sama ta Najeriya (FAAN) ta sauya wa jirage da tashin su waje cikin gaggawa daga sashin E na filin jirgin saman Murtala Muhammad (MMIA) sakamakon gobara da ta tashi.

Gobarar ta tashi ne da sanyin safiyar yau Alhamis bayan da aka samu hayaki a gadar E54.

Daily Trust ta rawaito cewa jami’an hukumar kashe gobara a filin tashi da saukar jiragen sama sun yi gaggawar daukar matakan shawo kan gobarar da ta katse wutar lantarki a tsohon bangaren tashi da saukar jiragen na kasa da kasa.

Sanarwa ta Musamman Daga Hukumar Samar da Ruwan sha ta Jihar Kano

Daily Trust ta ruwaito cewa tsohuwar tashar ta fuskanci matsalolin gobara, wanda hakan ya sa ake rufe ta lokaci zuwa lokaci.

Hukumar ta FAAN a cikin wata sanarwa da ta fito daga hannun daraktan hulda da jama’a da kare abokan mu’amala, Mrs Obiageli Orah, ta tabbatar da faruwar gobarar, inda ta ce cikin gaggawar jami’an kashe gobara na filin jirgin sun samu nasarar shawo kan lamarin.

Tsakananin zafi: Hukumomi a Kano sun ba da shawarwarin kare kai ga al’umma

Ta ce, “Da karfe 05:29 na safe, an gano hayaki yana ta turnukewa daga gadar E54, wanda hakan ya sa injiniyoyin lantarki suka katse wutar lantarki ga daukacin ɓangaren E.

“Rundunar ceto ta filin jirgin sama da masu kashe gobara (ARFFS) sun yi gaggawar zuwa wqjen, inda suka isa wurin da karfe 05:30 na safe.

“Abinda aka fara zargi shine tartsatsin wuta daga na’urar lantarki a matsayin musabbabin, amma ana ci gaba da gudanar da cikakken bincike don gano musabbabin tashin gobarar. Lamarin wanda ya rikide zuwa gobara, an shawo kan sa da karfe 06:41 na safe.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

An Dauke Shaikh Abduljabbar Daga Gidan Yari na Kurmawa Zuwa Wani Wuri – Yan uwansaba

Wani labari da ke yawo a kafafen sada zumunta...

Majalisu na neman sauya lokacin zabuka a Nigeria

Majalisar Dokoki Ta Ƙasa Ta Gabatar Da Kudirin Sauya...

Kungiyar Lauyoyi yan asalin jihar Kano sun mika korafi ga kasashen Amuruka Ingila da UN kan zargin kisan a Tudun Wada

Kungiyar Lauyoyin Yan Asalin Jihar Kano (National Forum of...

Da dumi-dumi: ASUU ta sanar da ranar da zata fara yajin aiki

Shugabancin Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya (ASUU) ta umurci...