Daga Rukayya Abdullahi Maida
Fitaccen jarumi a masana’antar kannywood Adam A zango yace baya jin dadin yadda wasu suke ganin laifi ko zagin wasu mutane guda 3 a kannywood da yace sun taimaka masa lokacin da yake cikin mawuyacin hali.
Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito cewa Adam Zango a Kwanakin baya ya lissafa sunayen wasu yan masana’antar Kannywood da yace ya taimake su Amma su sun ƙasa taimakonsa duk da mawuyacin halin da ya shiga.
” Bana jin dadi inga ana zagin Ali Nuhu da Abdul Amart da saboda dukkanin su sun taimaka masa a rayuwarsa musamman lokacin da ya fada mawuyacin hali sakamakon jarrabawar da Allah ya yi masa”.
Yanzu-yanzu: Gwamnatin Kano ta Rufe Wani Asibiti Mai Zaman Kansa Saboda Karya Doka
Adam Zango ya bayyana hakan ne a wani sabon bidiyo da ya saki a wannan rana ta lahadi a shashin shafinsa na shafukan sada zumunta.
Daga cikin wadanda Adam Zango ya ambaci sunansu har da Ali Nuhu wanda adamun yace yasan a baya sun sami matsala da shi, amma yanzu a matsayinsa na karami ya karɓi duk kura-kuran da yayi , sannan kuma yayi alkawarin cigaba da yiwa Ali Nuhu biyayya yadda ya dace.
” A matsayin na na karami na yarda a baya duk abubunwan da suka faru tsakanina da Ali Nuhu laifi nane, kuma na bashi hakuri komai ya wuce, kamar yadda na yi masa biyayya a baya yanzu Ina yi masa kuma zan cigaba da yi masa biyayya yadda ya dace”. A cewar zango
Yadda jarumar kannywood Aisha Humaira ta yi alkawarin magance matsalar ruwa a Kano
Dan gane da Abdul Amart kuwa shi ma Adam Zango yace baya Jin dadi ya ji ko ya ga ana zaginsa , saboda shi ma ya yi masa rana a dai-dai lokacin da yake cikin mawuyacin hali.
” Lokacin da na shiga wani hali Abdul Amart har gida ya zo ya same ni ya bani kyautar mota don haka bazan manta wannan alkhairin ba, Matsalar da ta faru tsakanina da shi Mun gyara ta yanzu komai ya wuce”. Inji zango
Sai wani Murtala Boloko wanda shi ma bana so na ga ana zaginsa ko a sanya hoton a rika zaginsa saboda shi ma ya tuna dani lokacin Ina cikin wani hali.
” Murtala Boloko har motarsa ya Sayar ya Kawo min kuɗin na yi amfani da su , don haka bazan manta da wannan karamcin da yayi min ba, har yanzu duk da zagina da kalaman da yake yi a kaina ban dora laifin da yayi min akan alkhairin da yayi min”. A cewar Adam Zango
Jarumin yace akwai mutane da dama da suka taimaka masa wasu da kudi wasu kuma da shawarwari, don haka yayi kira da yaransa da masoyansa da su daina zagin wadancan mutane da ya lissafa saboda yace ba zai taba bantawa da alkhairin da suka yi masa.