Iftila’i: Yadda Fadawar Wayar salula cikin masai ya yi Sanadiyar Mutuwa Uba da Da a Kano

Date:

Uba da Dansa tare da wani dan kai dauki sun rasu a kokarin dauko wata wayar hannu data fada cikin Shadda a garin Yar Gwanda dake karamar hukumar Tsanyawa, jihar Kano.

Tunda farko al’amarin ya faru ne, lokacin da mutumin mai suna malam Danjuma black, ya je bandaki biyan bukata, to sai wayarsa ta fada cikin Shaddar, Ashe ashe ajali ne ke kiransa.

Ganin haka tasa mutumin ya dauko tsani da zummar dauko wannan waya, ai kuwa shigarsa ke da wuya, ya kasa fitowa, kasancewar masan dama can tsohuwar rijiya ce, nan da nan aka kirawo dansa wanda matashi ne aka sanar da shi halin da ake ciki, abunka da soyayyar da da mahaifi, sai kawai ya shiga wannan masai domin kaiwa mahaifinsa dauki, ashe shi ma ajali ne ke kiransa, shi ma ya kasa fitowa.

Yanzu-yanzu: Gwamnatin Kano ta Rufe Wani Asibiti Mai Zaman Kansa Saboda Karya Doka

Ganin haka tasa aka kirawo wani mai harkar ginin rijiya tunda dama ya saba da irin wannan aikin, domin ya kai masu daukin gaggawa.

Da farko ya shiga cikin Shaddar harma ya samu nasarar dauko Dan Marigayin ya fito dasu amma baya motsi, sai kuma ya kara komawa ciki domin dauko Malam Dan juma wanda shi ne mahaifin matashin, to bayan ya yi yunkurin dauko shi domin fitowa, harma ya fara yo sama, sai shi ma ya yanke jiki suka sake fadawa cikin Shaddar tare.

Ba Zan Iya Aurar Wanda Baya Son Harkar Fim Ba – Asmee Wakeel

Ganin haka Yan garin suka yi gaggawar neman daukin jami’an kashe gobara, kasancewar an rasa wanda zai iya shiga ciki.

Bayan dauko su da jami’an kashe gobara suka yi, aka garzaya dasu zuwa Babban Asibitin Bichi, kuma a nan ne aka tabbatar da rai ya yi halinsa su duka ukkun.

Tuni aka yi masu sutura kamar yadda addinin musulunci ya yi tanadi, kamar yadda Mazaunin garin Sani Isma’il Yar Gwanda ya shaida man.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rasuwar Buhari: Majalisar Nigeria ta dakatar da duk aiyukanta

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Majalisar dokokin Nigeria ta dage zamanta...

Gwamnati ta baiwa ma’aikata hutu saboda rasuwar Muhammad Buhari

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Gwamnatin jihar Katsina karkashin gwamna Umar...

Bayan tura Kashim ya taho da gawar Buhari, Tinubu ya ba da umarnin sassauta Tutar Nigeria

Shugaban kasa Bola Tinubu ya bada umarnin ayi kasa...

Yanzu:yanzu: Tsohon shugaban Nigeria Buhari ya rasu

Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un!!! Allah yayi wa tsohon shugaban...