Daga Rukayya Abdullahi Maida
Falakin Shinkafi Amb. Yunusa Yusuf Hamza, ya yi kira ga gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi da su yi kira ga Yan kasuwa domin su sauke farashin kayayyakin su ko kuma su dauki matakan da suka dace akan su.
“Al’umma suna cikin wani hali tun lokacin da Dala ta tashi, mussaman yadda farashin kayan Masarufi sukai tashin gauron zabi a fadin Najeriya”.
Amb. Yunusa Yusuf ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da yayi wakilin Kadaura24 a Kano.
An janye ‘yan sandan da ke gadin tsohon gwamnan Kogi Yahaya Bello
“Talaka ya shiga wani hali na matsin rayuwa saboda yadda ake maganar Dala tayi tashin gauron zabi, sai gashi kuma yanzu Dala ta sauko, to shin mai ya kamata Yan kasuwar mu suyi a yanzu? Shi ne su sauke farashin kaya domin Talaka ya samu sauki”. Falakin Shinkafi
Yace duk dan kasuwar da zai yi ikirarin cewar Dala ta tashi zai kara kudin kaya, to ya kamata tunda yanzu Dala ta sauko ya sauke farashin kayansa idan har da gaske yake.
Gwamnan Kano ya chanzawa wasu daga cikin Kwamishinonin sa ma’aikatu
“Muna kira ga gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusif yadda ya zauna da Yan kasuwa a baya, da yanzu ma ya taimaka ya zauna da su domin talakawa su samu saukin halin da suke ciki”. A cewar Falakin Shinkafi
Hatta gwamnatin tarayya muna kira gare ta da tayi abinda ya dace akan Yan kasuwar mu, domin tabbatar da cewa sun sauke farashin kayansu.
A cewar Falakin Shinkafi “A lokacin da Dala ta kusa kaiwa 2000, Dan kasuwa zai siyo abu a naira 200 sakamakon tashin Dala, to a yanzu Dala ta sauko tana 1050 kuma yan kasuwa suna siyar da kaya akan Naira 195, wanda hakan bai kamata ba.