Hajjin Bana: Akwai yiwuwar NAHCON ta Mayar wa da Maniyata Rarar Kuɗi

Date:

 

Shugaban hukumar kula da aikin hajji ta Najeriya, Alhaji Jalal Ahmad Arabi ya ce akwai yiwuwar hukumar ka iya mayar wa maniyyata rarar kuɗin da suka biya sakamakon karyewar farashin dalar Amurka.

Alhaji Jalal Arabi ya shaida hakan ne a wata hira da kafar sadarwa ta DCL da ke intanet wadda kuma hukumar alhazan Najeriya ta wallafa a shafinta na X, ranar Alhamis.

“Idan misali ranar da muka yi shela dala tana naira 1000, sai ya zamana kai ranar da ka saka kudinka ka saka ne ranar da take naira 900, to ai ka ga akwai rarar naira 100. Wannan naira 100 ya kamata ma mu maida maka. Ba mu jira tana ta yin asa ba. To idan kuma ta ara yin sama fa?” In ji Jalal Arabi.

Kotu ta tabbatar da dakatar da Ganduje daga APC

Ya kara da cewa “indai da rai da lafiya kuma idan dai mu ne a kan kujerar to ba za mu zauna a kan hakkin kowa ba da iznin Allah. Za mu tabbatar mun biya wannan rarar.”

To sai dai shugaban hukumar ta Alhazan na Najeriya bai faɗi lokacin da za a mayar wa da maniyyatan rarar kuɗaɗen nasu ba.

A mafi yawancin lokuta dai hukumar ta Alhazai kan mayar wa alhazai rarar kudaɗen ne bayan kammala aikin Hajji.

A yanzu haka dai naira na ci gaba da samun tagomashi a kan dalar Amurka inda bayanai ke nuna farashin dala a kasuwar bayan fage na tsakanin naira dubu ɗaya da ƙasa da haka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin gida: Jam’iyyar APC ta Fara Tuhumar Kakakinta na Kano Ahmad S Aruwa

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jam'iyyar APC ta Mazabar Daurawa a...

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...