SANARWA TA MUSAMMAN!!!
Assalamu Alaikum.
A ƙoƙarinta na cigaba da ayyukan raya ƙasa da inganta walwalar jama’a, gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin jagorancin mai girma gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf ta bayar da umarnin aikin gina katafariyar Gadar ƙasa (Underpass tare da Gadar Sama, Flyover) a shataletalen Tal’udu.
A bisa buƙatar kammala wannan muhimmin aiki cikin lokacin da aka tsara, gwamnati ta ba wa Ɗan kwangila umarnin fara wannan aikin nan take.
Domin samun damar yin aiki cikin nustuwa da kwanciyar hankali, za a rufe sassan titin Muhammad Abdullahi Wase daga ranar Alhamis 18/4/2024.
A bisa buƙatar sauƙaƙa zirga-zirga ga masu ababen hawa, ma’aikatar ayyuka da gidaje ta jihar Kano ta samu nasarar samarwa tare da gyaran hanyoyin da za a yi amfani da su domin kyaucewa wurin da aka rufe.
Kotu ta tabbatar da dakatar da Ganduje daga APC
An samar da titunan yanke ta cikin unguwanni kamar haka:
1- Titin Muhammad Abdullahi Wase (Rahama Street zuwa titin Aminu Kano (W.A.A RANO Filling Station).
2- Titin Aminu Kano zuwa titin Muhammad Abdullahi Wase (Kusa da makarantar Adamu na Ma’aji).
3- Titin Muhammad Abdullahi Wase (Layin Nufawa zuwa titin Aminu Kano, layin Mai Tangaran).
4- Titin Aminu Kano (Shaho Street zuwa titin Muhammad Abdullahi Wase).
Haka kuma ana shawartar masu ababen hawa da su nisanci wurin da ake gudanar da wannan katafaren aiki idan ba ya zama dole ba, domin samun zirga-zirga cikin nutsuwa kuma rage cunkoso.
Tinubu na son in ci gaba da zama shugaban APC – Ganduje
Gwamnatin jihar Kano tana ƙara neman goyon baya tare da haɗin kan jama’a domin samun nasarar wannan aiki da zai inganta rayuwarmu, bunƙasa kasuwanci tare da kyautata zirga-zirga cikin yanayi mai sauƙi.
Muna godiya tare da jinjina ga jama’ar Kano bisa soyayya, addu’o’i, goyon baya tare da ƙwarin guiwa da ku ke ba wa mai girma gwamna da gwamnatinsa.
Mun gode ƙwarai da gaske.
Sign:
Engr Marwan Ahmed Aminu, MNSE Hon. Commissioner, Ministry of Works and Housing