Daga Rukayya Abdullahi Maida
Babban layin wutar lantarki ta na ƙasa ya sake sauka, kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito .
Babban layin wutar lantarkin ya sauka ne da misalin karfe 2:42 na safiyar yau Litinin, inda karfin wutar ya ragu zuwa megawatt 64.70 kacal.
Kamfanin samar da wutar lantarki guda daya ne kawai ke aiki kamar yadda bayanai daga cibiyar sarrafa aikin rarraba wutar lantarki (ISO), reshen kamfanin rarraba wutar lantarki na kasa suka nuna.
Adam A Zango ya yi suka mai zafi tare da zargin yan masana’antar Kannywood kan halin da yake ciki
Wannan shi ne karo na shida da babban layin ya sauka a cikin wannan shekara 2024 da muke Ciki.
Daily Trust ta ruwaito cewa, da misalin karfe 8 na safiyar yau Litinin, sabbin bayanai da cibiyar ta ISO ta fitar sun nuna cewa a halin yanzu tashar tana samar da wutar lantarki mai karfin megawat 266.50 daga Okpai, Geregu da Ibom.
EFCC ta yi Martani game da labarin wanke Ministar Jin kai Bette Edu
Da yake tabbatar da saukar layin a cikin wata sanarwa, kfanin rarraba wutar lantarki na Jos ya ce: “Katsewar da ake fuskanta a halin yanzu a cikin jihohinmu ya samo asali ne daga saukar babban layin wutar lantarki na kasa. Hakan kuma ya afku ne da sanyin safiya da misalin karfe biyu na yau litinin, 15 ga watan Afrilu 2024, wanda hakan ya sa aka rasa wutar lantarki a kasar.”
Shugaban sashen hulda da jama’a na Kamfanin, Dakta Friday Adakole Elijah, ya bayyana fatan cewa za a shawo kan lamarin nan ba da dadewa ba.